An kama wani mutum da bindigogi AK 47 guda 15 a Bauchi
Wani mutum mai suna Bello dankogol ya shiga hannun jami’an tsaron kasa (SSS) bayan da wasu jami’an tsaro suka kama shi dauke da bindigogi kirar AK 47 guda 15 a cikin motarsa a BauchiKakakin Hukumar SSS na Bauchi, Kabiru Abdulsamad, ya ce an kama Bello dankogol ne sakamakon samun rahoton sirri a ranar Juma’a da […]

Wani mutum mai suna Bello dankogol ya shiga hannun jami’an tsaron kasa (SSS) bayan da wasu jami’an tsaro suka kama shi dauke da bindigogi kirar AK 47 guda 15 a cikin motarsa a Bauchi
Kakakin Hukumar SSS na Bauchi, Kabiru Abdulsamad, ya ce an kama Bello dankogol ne sakamakon samun rahoton sirri a ranar Juma’a da ta gabata.
Abdulsamad ya ce wanda ake zargin ya dauko bindigogin ne da aka boye a cikin motarsa kirar Toyota kirar Solara mai lambar Legas, HM 605 EKY lokacin da aka kama shi. Ya ce dankogol ya yi fataucin bindigogi 47 tsakanin Yulin bara da Janairun bana ga kungiyoyin masu aikata miyagun ayyuka. Kuma dankogol ya yi ikirarin safarar bindigogi ga masu aikata miyagun ayyuka a Jos inda ya rika kawo makaman daga garin Gambaru da ke Kamaru ta bin hanyar Maiduguri zuwa Bauchi zuwa Filato, kamar yadda kakakin na SSS ya fada.
Abdulsamad ya ce “Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa wannan ne karo na shida da yake fataucin bindigogi daga Maiduguri zuwa Filato,” don haka ya bukaci jama’a su tallafa wa jami’an tsaro a yakin da suke yi da ayyukan miyagu.
“Gabatar da wanda ake zargin gabanku shi ne domin a sanar da ’yan Najeriya su san cewa rikice-rikicen da suke faruwa a sassan kasar nan ba su da alaka da addini ko siyasa,” inji shi.
dankogol ya tabbatar da cewa wannan ne karo na shida da yake fataucin bindigogi daga Kamaru zuwa Filato, kuma ana aikensa ne a biya shi Naira dubu 100 a kowane sawu.
Da aka tambaye shi kan yadda yake tsallake shingayen jami’an tsaro a kan hanyoyi, sai ya ce, “Nakan sanya bindigogin ne a can karkashin kasar ma’ajiyar kaya, kuma a lokacin da na je wurin duba ababen hawa sukan duba saman ma’ajiyar ne kawai, yayin da wasu kan ce in wuce ba tare da sun duba ba.”