An kama wani soja da korararrun sojoji kan yin sojan gona a Legas

Sashe na 81 na rundunar sojan Najeriya da ke jihar Legas ta kama mutane 13 har da wani soja da ya gudu daga bakin aiki da wandanda aka kora daga aiki sakamakon aikata laifin sojan gona. Ta bayyana cewa ta kama wadanda ake zargin sanye da kayan sojoji yayin da suke cin zarafin jama’a  tare […]

An kama wani soja da korararrun sojoji kan yin sojan gona a Legas

Sashe na 81 na rundunar sojan Najeriya da ke jihar Legas ta kama mutane 13 har da wani soja da ya gudu daga bakin aiki da wandanda aka kora daga aiki sakamakon aikata laifin sojan gona.
Ta bayyana cewa ta kama wadanda ake zargin sanye da kayan sojoji yayin da suke cin zarafin jama’a  tare da yi musu barazanar da aikin soja.
 
Wadanda ake zargin  wadanda duk maza ne an kama su ne a sassa da dama na jihar Legas da Ogun.
 
Shugaban sashen rundunar ta 81, Birgediya Janar Hamisu Hassan shi ne ya gabatar da su jiya a madadin kwamandan rundunar Enobong Udoh a hedikwatar  rundunar da ke yankin Kofo Abayomi.
 
Daga cikin wadanda aka kama akwai wasu bata-gari da ke taimakawa masu laifin ta hanyar yi musu katin shaida da samar musu da kakin soja da sauran kayan jami’an tsaro.
 
Sun hada da Emmanuel Anthony da Abdullahi Mubarak da Ibeh Gabriel Emeka da Olusunkanmi Olamide da Godwin Emmanuel da korarren soja Ahmed Yahaya da Ale Ayokunle da Robert Danang da Kofur Abubakar da korarren soja Ibrahim Isah da Monday Oga da Emeka Stephen da kuma Bala Gabariel.