An kama wasu ’yan Boko Haram a Chadi
An kama wani jigo a kungiyar Boko Haram a kasar Chadi, kamar yadda babban mai shigar da kara a kotu a birnin N’Djamena na kasar Chadi, Alghassim Khamis, ya bayyana ranar Talata. Mutumin mai suna, Baana Fanay, wanda ake yi wa lakabi da sunan Mahamat Moustapha. Ana zargin yana safarar makamai tsakanin kasashen Kamaru da […]
An kama wani jigo a kungiyar Boko Haram a kasar Chadi, kamar yadda babban mai shigar da kara a kotu a birnin N’Djamena na kasar Chadi, Alghassim Khamis, ya bayyana ranar Talata.
Mutumin mai suna, Baana Fanay, wanda ake yi wa lakabi da sunan Mahamat Moustapha. Ana zargin yana safarar makamai tsakanin kasashen Kamaru da Chadi da kuma Najeriya. Har ila yau, ana zarginsa da tilasta wa yara kanana shiga aikin soja.
Babban mai shigar da karar ya ce wani binciken da aka yi a gidan wannan mutum da ke birnin N’Djamena, ya gano cewa wasu manyan makamai biyar da wayoyin hannu na sadarwa da layukan waya daban-daban fiye da guda 50 har ma da wasu na kasashen ketare.
Babban mai shigar da karar ya ce jami’an tsaro na ci gaba da farautar wani mutum daban da ake fatan cewa zai shiga hannu hukuma nan ba da dadewa ba.
Hukumomi sun ce bayanai da suka tatso daga Baana bayan ya shiga hannu, ya kai ga gano wata mabuyar ’yan kungiyar Boko Haram a unguwar Diguel Dinguessou, inda aka kubutar da maza bakwai da mace guda da yara kanana biyu.
Har ila yau, lokacin da jami’an tsaro suka yi dirar mikiya a unguwar, wani dan kungiyar ya tayar da wani abin fashewa. Lamarin da ya hallaka jami’an tsaro biyar da kuma wasu mutane shida daga bangaren mayakan kungiyar.
Wani mutum da ake kyautata zaton cewa yana daya daga cikin masu daukar nauyin kungiyar ne shi ma ya shiga hannu. Wannan ya sa masana suke hasashen cewa binciken da za a gudanar akan wadannan mutanen duka zai ba da damar gano wasu sabbin hanyoyin da wannan kungiyar take bi wurin ci gaba da kai hari.
Tun ranar 15 ga watan Yuni, wato lokacin da aka kai tagwayen hari a birnin N’Djamena wanda ya hallaka akalla mutum 38, ya kuma raunata sama da 100. Hakazalika, jami’an tsaro sun kama mutum 74 da ake zargi da hannu a cikin wadannan hare-haren.
Daga bisani kuma sai da ta kai ga jami’an tsaro suna kama duk wasu baki da suke zaune a birnin N’Djamenan ba bisa ka’ida ba. A cikinsu a kwai ‘yan Kamaru, ’yan Najeriya da kuma tarin wasu baki da suka fito daga yankin Yammacin Afirka. Fiye da ’yan Kamaru 300 ne jami’an tsaron Chadi suka tasa keyarsu zuwa gida. A yayin da kuma ’yan Chadi kusan su 50 ne jami’an tsaron Kamaru suka koro gida a wani mataki na ramuwar gayya.
Hakan ya sa masana suke ganin irin wannan halin na tasa keyar jama’ar kasashen juna ka iya haifar da rashin jituwa a tsakanin tsakaninsu kasashen biyu. Kodayake, doka a Kamaru da Chadi ba ta yarje ma wani dan wata kasa da ya zauna a daya daga cikin kasashen na wani lokaci mai tsawo ba tare da sanar da jami’an tsaro masu kula da shiga da ficen jama’a ba.