An kama wata mata da buhu 13 na tabar wiwi
Tuni rundunar ta fara bincike a kan matar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, sun kama wata mata mai shekaru 57 da buhu 13 da ake zargin suna ɗauke da tabar wiwi.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Bright Edafe, ya ce jami’an QRS ne suka kama matar a Warri da ke Jihar Delta.
- ’Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 7, sun ƙwato N7.5m a Katsina
- Sallah: Farashin raguna ya kai N700,000 a Kano
Ya bayyana cewa a ranar 22 ga watan Mayu, 2026, jami’an rundunar sun tsayar da wani babur mai ƙafa uku domin bincike a kan titin Esisi da ke Ƙaramar Hukumar Warri ta Kudu.
A yayin binciken ne jami’an suka gano buhu 13 ɗauke da abubuwan da ake zargin tabar wiwi ne.
An kama matar nan take.
Edafe ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano inda ta samo kayan da kuma inda ake kai su.