An kama wata mata da hodar koken cikin al’aurarta
Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wata mata mai sana’ar sayar da abinci a kasuwar Ajamgbadi a birnin Ikko, mai kimanin shekaru 36, mai suna Chinelo Okorom Lynnet da ta boye hodar koken mai nauyin giram 685 cikin al’aurarta.Jami’an hukumar sun cafke ta ne lokacin da ta shigo jirgi daga […]

Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wata mata mai sana’ar sayar da abinci a kasuwar Ajamgbadi a birnin Ikko, mai kimanin shekaru 36, mai suna Chinelo Okorom Lynnet da ta boye hodar koken mai nauyin giram 685 cikin al’aurarta.
Jami’an hukumar sun cafke ta ne lokacin da ta shigo jirgi daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha (Ethiopia), kamar yadda kwamandan rundunar mai kula da tashar jirgin saman Murtala Mohammed, Malam Hamza Umar ya bayyana cewa matar ta hadiye wasu kulli, wasu kuma ta saka su a al’aurarta.
Sa’ilin da ake mata tambayoyi, bayan ta fitar da kulle-kullen, ta ce tana sayar da abinci ne a kasuwar Ajamgbadi, kafin mijinta ya tsere ya bar ta da yara kanana daga bisani maigidan da take haya cikinsa ya kore ta kuma a lokacin ba ta san inda za ta ba, sai ta hadu da mutumin da ya aike ta da wannan mugunyar haja.
Ta ce ta nemi ki, amma mutumin ya yi mata barazanar daukar matakin fitar da kudin da ya kashe kanta, lamarin da ya firgita ta har ta amince.
Shi ma wani mai suna Oguike Franklin mai shekaru 33, an kama shi ne da tabar wiwi da yake kokarin sawa cikin jirgin KLM sa’ilin da ake masa lodin kayansa na shafe-shafe da za a kai Paramaribo a Amurka ta Kudu.
Da aka kama shi, sai ya ce wani abokinsa ne ya shigar da shi cikin harkar a lokacin da jarinsa ya karye, a yayin da yake sayar da kayan lantarki a kasuwar Aba. Amma shi ko wani dan kasar Pakistan, mai shekaru 19, mai suna Iftikihar Mohammed Arslan an kama shi ne da tabar ‘heroin’ mai nauyin giram 25,400, wadda aka kiyasta kudinta zai kai Naira miliyan 228, ya sauka filin jirgin saman Murtala Mohammed din ne daga birnin Lahore.
Ya ce shi dan makaranta ne a kwalejin Punjab, ya zo Najeriya ne da niyyar yawon bude ido da niyyar share sati guda a unguwannin Ikoyi da bictoria Island.
Malam Hamza ya ce duk wadannan bayan sun gama bincikensu za su mika su kotu.