An kama wata mata da kwayoyi dubu da 600

Wata fasinjar jirgin sama da aka kama da kwayoyin turamol (tramadol) a dubu da 600 a akwatinta na tafiya a Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce don amfanin  kan ta,  domin a cewarta, ‘likita ne ya rubuta mata. Kotun hukunta nmasu aikata miyagunb laifuka ta Abu Dhabi ta sameta da laifin shigowa kasar daga Masar da […]

An kama wata mata da kwayoyi dubu da 600

Wata fasinjar jirgin sama da aka kama da kwayoyin turamol (tramadol) a dubu da 600 a akwatinta na tafiya a Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce don amfanin  kan ta,  domin a cewarta, ‘likita ne ya rubuta mata.

Kotun hukunta nmasu aikata miyagunb laifuka ta Abu Dhabi ta sameta da laifin shigowa kasar daga Masar da jakkarta cike da kwayoyin Turamol a filin jirgin saman kasar.

Jami’an kotun sun nuna hujjojin da suka tabbatar an kama matar a watannin da suka wuce, inda jami’an tsaro suka kama kwayoyin maganin.

Masu gabatar da kara sun bayyana yadda binciken jami’an hana fasakwauri suka bankado kwalayen magungunan da ke dauke da kwayoyin dubu da 600.

Matar da ta taso daga filin jirgin saman Alkahira, gwajin jininta ya nuna cewa tana shan kwayoyin maganin. Matar dai ta musa laifukan safarar kwaya da aka tuhumeta, in da ta doge kan cewa ita ta yi safar magungunan ne don amfganin kanta.

Da alkalin yanemi hujjar da ta hanata neman magani a Hadaddyar Daular Larabawa don nan ne take da zama, sai ta ce, ‘maganin cutarta kawai sai ta koma gida a kasarta ta haihuwa.’

 

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi