An kama wata mata da ta yi garkuwa da yarinya a Legas

Wata mata ’yar kimanin shekaru 20 mai suna Ajoke Owolabi, wacce ta yi garkuwa da yarinya ’yar kimanin shekara 7 ta shiga komar ’yan sanda. A cewar kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun, ASP Abimbola Oyeyemi, matar ta yi garkuwa da yarinyar ne har tsawon kimanin watanni 19, inda yarinyar ta kuɓuce bayan da […]

An kama wata mata da ta yi garkuwa da yarinya a Legas

Wata mata ’yar kimanin shekaru 20 mai suna Ajoke Owolabi, wacce ta yi garkuwa da yarinya ’yar kimanin shekara 7 ta shiga komar ’yan sanda.

A cewar kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun, ASP Abimbola Oyeyemi, matar ta yi garkuwa da yarinyar ne har tsawon kimanin watanni 19, inda yarinyar ta kuɓuce bayan da aka rufe ta a ɗaki ta tafi biki a Abekuta. Bayan da yarinyar ta fito ne aka sami wani mutum da ya kai ta gidan mahaifanta.

Asirin matar ya cika ne bayan da ta zo wucewa ta gidan su yarinyar, a daidai lokacin da ta yi ido biyu da ita, nan take ta yi kwarmaton cewa ga matar da ta sace ta. Nan take aka kama ta. Kakakin ya ƙara da cewa da fari matar ta musanta cewar ita ce ta yi garkuwa da yarinyar, inda ta ce ba ta taɓa ganin ta ba, har sai da yarinyar ta ambaci sunanta, ta ce Anti Ajoke aka kuma tabbatar da sunanta ke nan, kafin da ga bisani ta amsa laifinta. Ta ce ta yi garkuwa ne da yarinyar a wani gida da ke Oshodi a Legas.

Tuni dai Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin tasa ƙeyarta zuwa sashin rundunar na musamman da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane domin ci gaba da bincike.