An kama ’yan 419 da sunan Sarkin Katsina
Dubun masu damfarar manyan mutane da sunan Sarkin Katsina ta cika bayan ’yan sanda a jihar sun kama su. Mutanen na amfani da sunan Majalisar Masarautar Katsina suna tura sakonnin waya ga manyan mutane na neman su tura kudade zuwa wani asusun banki da sunan gudunmuwa ga Masarautar. Kakakin ’yan sandan Katsina, SP Gambo Isah […]
Dubun masu damfarar manyan mutane da sunan Sarkin Katsina ta cika bayan ’yan sanda a jihar sun kama su.
Mutanen na amfani da sunan Majalisar Masarautar Katsina suna tura sakonnin waya ga manyan mutane na neman su tura kudade zuwa wani asusun banki da sunan gudunmuwa ga Masarautar.
Kakakin ’yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya ce mutanen da suka riga suka cuci wasu manyan mutane “na fakewa ne a matsayin Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo, Sallaman Katsina da cewa Masarautar na neman taimako domin aurar da ’yan mata marayu”.
Gambo Isah ya ce kafin asirinsu ya tonu, ’yan damfarar da suka hada da dan Jihar Katsina da dan Jihar Nasarawa, sun tura irin wadannan sakonni ga wasu manyan mutane da suka hada da:
Farfesa Ango Abdullahi da Janar Muhamadu Buba Marwa da Hon. Chairman Abdullahi Adamu Candido da Umaru Ajiya – NNPC da Manjo M. K. Yusuf – Legas da Sanata Sa’idu Alkali da Darekta Janar na hukumar NYSC – Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim da sauransu.