An kama ’yan Arewa 400 a Bayelsa

Jami’an Hukumar Shigi da Fici a Jihar Bayelsa sun kama ’yan Arewa 400 a Yenagoa babban birnin jihar, bisa zargin baki ne ’yan kasashen waje da zamansu a jihar ka iya zama barazana ga harkokin tsaro.Kamen wanda hukumar ta kaddamar a ranar Litinin akasarin wadanda aka kama ’yan asalin jihohin Kano da Jigawa ne da […]

An kama ’yan Arewa 400 a Bayelsa
An kama ’yan Arewa 400 a Bayelsa

Jami’an Hukumar Shigi da Fici a Jihar Bayelsa sun kama ’yan Arewa 400 a Yenagoa babban birnin jihar, bisa zargin baki ne ’yan kasashen waje da zamansu a jihar ka iya zama barazana ga harkokin tsaro.
Kamen wanda hukumar ta kaddamar a ranar Litinin akasarin wadanda aka kama ’yan asalin jihohin Kano da Jigawa ne da kuma kalilan daga Jamhuriyar Nijar, suna zaune ne a jihar a tsawon lokaci suna gudanar da kananan sana’o’i da suka hada da aikin gadi da wanke talakma da kuma yankan farce.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas ta kama mutum 270 a cikin motoci 17 da suka fito daga Jihar Jigawa domin yin cin ranin da suka saba kamar yadda suka ce suna zuwa kowace shekara.
Wani mai suna Rabi’u Bayelsa da ya tsallake wa kamun ya shaida wa Aminiya cewa: “Muna zaune lafiya wasunmu ma sun dawo daga kasuwancinsu ke nan sai muka ga jami’an hukumar sun zo sun ce sun kama mu suna son su tantance mu saboda dalili na tsaro. Mafi rinjaye daga cikinmu duk Kanawa ne da kuma mu ’yan asalin Jihar Jigawa sai kuma wasu ’yan Nijar biyu da aka kama amma su an sake su bayan an same su da takardu da suka kamata.”
A hira da manema labarai kakakin hukumar shigi da fici ta kasa Chukwu Emeka Obua ya tabbatar da an yi kamen, inda ya ce hakan abu ne da suka saba gudanarwa lokaci zuwa lokaci a sassa daban-daban na kasar nan.
Kakakin hukumar shige da ficen ya ce bayan tantancewa an saki mutum 100 daga cikinsu.
Shi dai wannan al’amari ya zo ne a daidai lokacin da ake yawan kama ’yan Arewa, bisa zarginsu da kasancewa barazana ta fuskar tsaro ko kuma ’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram.