An kama ‘yan bangar siyasa 10 da suka tada rikici a Jigawa
Hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa sun ce, sun kama wadanda ake zargin ‘yan bangar siyasa ne 10 da suka tada rikici a wani taron siyasa, inda aka raunata mutum 4 a karamar hukumar Gwaram da ke jihar. Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar SP Abdu Jinjiri ne ya sanar da hakan yayin […]
Hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa sun ce, sun kama wadanda ake zargin ‘yan bangar siyasa ne 10 da suka tada rikici a wani taron siyasa, inda aka raunata mutum 4 a karamar hukumar Gwaram da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar SP Abdu Jinjiri ne ya sanar da hakan yayin tattaunawar da Kamfanin dillancin labarai NAN ya yi da shi a Dutse babban birnin jihar yau Talata.