An kama ’yan bindiga 5 bayan musayar wuta da ’yan sanda a Abuja

An kama ’yan bindigar bayan musayar wuta da su a dajin da ke tsakanin yankin Dei-Dei da Gwagwa da ke wajen garin Abuja

An kama ’yan bindiga 5 bayan musayar wuta da ’yan sanda a Abuja

’Yan sanda sun kama ’yan bindiga guda biyar bayan musayar wuta da su a Yankin Babban Birnin Tarayya.

An kwato bindigogi kirar AK-47 da wata kuma a hannun ’yan bindigar da aka kama a dajin da ke tsakanin yankin Gwagwa  Dei-Dei da ke wajen garin Abuja.

Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ya sanar a safiyar Alhamis cewa ’yan bindigar sun shiga hannu ne a samamen kwana uku da rundunar ta gudanar a yankin.

Ya ce bayan samun bayanai kan ayyukan bata-garin ne ’yan sanda suka yi dirar mikiya a maboyar ’yan bindigar, inda bayan musayar wuta suka kamo su kan garkuwar da aka yi da mutane ranar 12 ga watan Yuni, 2024.

Ana zargin sun karbi kudin fansa miliyan N12 daga iyalan wasu daga cikin mutanen da suka sace, duk da cewa masu garkuwar sun kashe biyu daga cikin mutanen da suka sace.

A cewar Igwe, ’yan bindigar, wadanda duk matasa ne sun amsa laifin da ake zargin su na addabar yankin da sace mutane domin karbar kudin fansa.

CP Igweh, ya ce da zarar rundunarsa ta kammala bincike za ta gurfanar da su a kotu domin su girbi sakamakon abin da suka shuka.

Sannan ya ba wa jama’a tabbacin yin aiki tukuru domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar.

Daga nan ya ja hankalinsu da su kasance masu lura tare da kiran wadannan lambobin kar-ta-kwana a duk lokacin da bukatar hakan ya taso: 08032003913, 08028940883, 08061581938, and 07057337653.

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai