An kama masu garkuwa da mutane a cikin kasuwa a Kebbi
An kama mutanen da ake zargin ne a Kasuwar Bagudo inda aka ƙwace makamai a hannunsu
Wasu mutum uku sun shiga hannu kan zargin yin garkuwa da wani dattijo mai shekara 55 a Jihar Kebbi.
Kakakin ’yan sanda a jihar, SP Bashir Usman, ya ce an kama mutanen ne a Kasuwar Bagudo inda aka ƙwace makamai ƙiran gida hannunsu.
Sanarwar da ya fitar ta ce ana zargin mutanen sun yi garkuwa da mutumin ne daga ƙauyen Bani Koso da ke Ƙaramar Hukumar Shanga, kafin dubunsu ta cika.
SP Bashir ya bayyana cewa an damƙa waɗanda ake zargin—Abubakar Muhammadu, Abdullahi Majo, da Ali Alhaji Jemu—ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) da ke Birnin Kebbi, bisa umarnin Kwamishinan’Yan Sanda na jihar, Umar Mohammed Haɗejia.
- Magidanta 96 sun yi watsi da ’ya’yansu babu kulawa a 2025 a Gombe — NHRC
- An kama ɗan fashi da ake zargi da ƙwato daloli na bogi
Ya ce, da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu, yana mai kira ga. jama’a ta su taimaka wa jami’an tsaro da rahoton duk wani motsi da ba su yara da shi ba.