An kama ’yan bumburutu 13 kan zargin kashe dan kasuwa a Abuja

Rundunar ’Yan sandan Abuja na ci gaba da bincike a kan wasu matasa 13 bisa zarginsu da kashe wani dan kasuwa ta hanyar duka da zuba masa ruwan zafi.  Matasan wadanda dukkansu ’yan bumburutu ne da ke sayar da man fetur a bakin titi a yankin Garki da ke birnin na tarayya, Aminiya ta samu […]

An kama ’yan bumburutu 13 kan zargin kashe dan kasuwa a Abuja
An kama ’yan bumburutu 13 kan zargin kashe dan kasuwa a Abuja

Rundunar ’Yan sandan Abuja na ci gaba da bincike a kan wasu matasa 13 bisa zarginsu da kashe wani dan kasuwa ta hanyar duka da zuba masa ruwan zafi. 

Matasan wadanda dukkansu ’yan bumburutu ne da ke sayar da man fetur a bakin titi a yankin Garki da ke birnin na tarayya, Aminiya ta samu labarin cewa da farko an tsare su ne a babban ofishin ’yan sanda na Garki, bayan an kama su daga bisani aka garzaya da su sashin yaki da fashi da makami da miyagun ayyuka (SARS), inda a ke ci gaba da yi musu bincike.
A zantawarsa da Aminiya a farkon wannan mako, wani dan uwan marigayin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce marigayin mai suna Yusuf Isma’ila mai shekara 33 da ke tireda a wani wuri da ake kira Bakasi da ke yankin na Garki, kisan nasa ya biyo bayan sabani ne da ya samu da wani dan garinsu mai suna Bashir Ahmad da ke bumburutu bayan ya ba shi Naira dubu 29 da nufin ya ajiye masa zuwa wayewar gari don gudun faduwar kudin a wajensa, kasancewar yana guje-guje a lokacin da yake sayar da mai a bakin titi a yankin na Garki.
dan uwan marigayin ya ce sai dai a lokacin da dan bumburutun ya dawo wajen marigayin kashegari don amsar kudin, marigayin ya shaida masa cewa kudin sun salwanta tare da nasa Naira dubu Bakwai bayan an yi masa sane a aljihunsa cikin dare a lokacin da yake barci.
Ya ce sai dai bayanin nasa bai gamsar da Bashir ba, kuma a dalilin haka dan uwan nasa ya ba shi baki na ya yi hakuri zuwa kwana biyar, zai nemo kudi don ya mayar masa, amma ya nuna bai ma yarda da batan kudin ba, sannan ba zai amince da jinkirta mayar masa da kudin ba, inda ya yi masa barazanar zai dauki mataki matukar bai ba shi kudinsa ba.
“Da misalin karfe 7:00 na dare a ranar, lokacin ana ruwan sama sai Bashir ya zo inda dan uwana ke yin kasuwanci tare da wasu abokan harkarsa da ya gayyato, suka kama shi suka daure shi a jikin wata bishiya wasu na duka wasu na zuba masa ruwan zafi. Da farko sun dauka suma ya yi, amma daga bisani ya bayyana a gare su cewa ya rasu ne, sai suka dauke shi suka jefa shi a wani wuri inda daga bisani muka gano gawarsa a cikin daren bayan samun labarin, sai muka shigar da kara a babban ofishin ’yan sanda na Garki,” inji shi.
Babban Jami’in ’Yan sanda na Garki (DPO) Mamman J., ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu, inda ya ce sun mika babban wanda ake zargin da sauran matasan su 12, ga babbar hedkwatarsu ta Abuja don ci gaba da bincike.