An kama ’yan fashi 2 da suka sato mota
Rundunar ’yan sandan ta yi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota.
Jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Ogun sun yi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi ’yan fashi da makami ne, wadanda suka hada da Kenneth Akpa da Adebayo Michael bisa zargin satar mota a Jihar Legas.
Rundunar ’yan sandan Gundumar Iperu ta kame wadanda ake zargin ne bayan samun labarin cewa, wata mota da ake zargin sato ta aka yi kirar Toyota Corolla 2008 an gansu ne a wani garejin kanikawa da ke kan titin Ogere/Iperu inda ’yan fashin ke kokarin gyara ta.
- Kira ga Shugaban Kasa Buhari
- Kusan rabin kafafen yada labaran Afghanistan sun rufe harkokinsu – Bincike
Kakakin rundunar ’yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai a makon da ya gabata cewa, Shugaban ofishin ’yan sandan yankin Iperu DPO ya tura jami’ansa zuwa wurin da aka kama wadanda ake zargin biyu tare da kwato motar mai lamba MUS 599 GB.
A cewarsa, an tuntubi mai motar, mai suna James John Ushahemba, mazaunin garin Ahoyaya da ke Legas, kuma ya isa Iperu.
Ushahemba ya bayyana cewa: “Wasu mutum biyu dauke da makamai ne suka kai masa hari a gidansa a ranar 20 ga Disamba, 2021, da misalin karfe 1:30 na tsakar dare.
“Ya kuma kara da cewa, ’yan fashin sun yi masa fashin motarsa kirar Toyota Corolla, tare da wayoyin sadarwarsa uku da tsabar kudi Naira dubu 30 ta hanyar yi masa barazana da bindiga.”