An kama ‘yan fashin da suka guntile hannun dan kasuwa bayan kwace masa Naira miliyan 3

’Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wadansu mutum biyu masu suna Danneri Mohammed da Abubakar Woru bisa zarginsu da guntule hannun wani mai suna Abdurraheem Abdul Kareem tare da kwace masa makudan kudi.                                                                                                                                                    Wadanda ake zargin sun furta da bakinsu cewa, su ne suka sassari jikin dan kasuwar mai Abduraheem Abdul Kareem tare da […]

An kama ‘yan fashin da suka guntile hannun dan kasuwa bayan kwace masa Naira miliyan 3

’Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wadansu mutum biyu masu suna Danneri Mohammed da Abubakar Woru bisa zarginsu da guntule hannun wani mai suna Abdurraheem Abdul Kareem tare da kwace masa makudan kudi.                                                                                                                                                    Wadanda ake zargin sun furta da bakinsu cewa, su ne suka sassari jikin dan kasuwar mai Abduraheem Abdul Kareem tare da guntile hannunsa da kwace fiye da Naira miliyan 3 daga hannunsa.

Da yake nuna wadanda ake zargi da  fashin ga manema labarai a Ibadan, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu ya ce, a ranar 25 ga Maris da ya gabata ne wadanda ake zargin suka yi wa dan kasuwar mai harkar canjin kudade kwanton-bauna a kauyen Ayemojuba kusa da garin Saki inda suka yi amfani da adduna wajen sarar sassan jikinsa tare da guntile zira’in hannunsa bayan sun kwace masa Naira miliyan 3 da dubu 100, suka jefar da shi a daji suka yi tafiyarsu. “Wadansu mutane ne suka ceci dan kasuwar da suka kai shi zuwa asibiti tare da kai rahoton aukuwar lamarin ga ayarin yaki da fashi da makami (SARS) na ’yan sanda da ke Saki.

Bayan samun rahoton ne ’yan sandan SARS suka fara bincike, inda suka gano maboyar wadanda ake zargin a garin Ilesabaruba a Jihar Kwara suka kama so,” inji Kwamishinan.

Ya kara da cewa, “Amincewa da aikata danyen aikin da wadanda ake zargin suka yi tare da muhimman bayanan da suka yi za su taimaka wajen kama sauran abokan aikinsu da suka tsere.”

Daya daga cikin wadanda ake zargin, Abubakar Woru ya shaida wa Aminiya cewa: “Gaskiya ne muna rike da bindiga guda daya da adduna da wukake lokacin da muka tare wannan mutum a kan hanya muka sassare shi muka guntile hannunsa muka karbe kudinsa.  Kuma kudin da muka kwace Naira miliyan daya da dubu 200 ne.”

Abubakar Woru ya ce “Mun kashe kudin duka kuma bindigar da muka yi amfani da ita a lokacin mun same ta ce daga wani abokinmu da ya kawo ta daga kasar Benin. Wannan shi ne karo na farko da aka yi fashi da makami tare da ni.”

Kwamishina Shina Olukolu ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin yanke musu hukuncin da ya dace.