An Kama ’Yan Fashin Da Suka Kashe ’Yar NYSC A Binuwai
Sun kashe Irene a lokacin da suke kokarin kwace kwanfiyutarta
’Yan sanda sun kama ’yan fashin da ake zargi da harbe wata mai yi wa kasa hidima har lahira a garin Makurdi na Jihar Binuwai.
’Yan fashin sun kashe Irene Chioma Emmanuel, wadda ke aikin hidimar ƙasa ne a lokacin da suke kokarin kwace kwanfiyutarta, a kan titin Naka-Makurdi da ke Makurdi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya shaida wa ’yan jarida a hedikwatar rundunar cewa ’yan fashin sun amsa cewa su ne suka kashe Irene kuma su ne suka addabi yankin da yin fashi da makami.
- Yadda daɗin zama ke haɗa auratayya tsakanin ’yan Arewa da ƙabilun Kuros Riba
- Tsadar rayuwa: Nama ya gagara, an koma cin awara
Adesina ya ce bayan samu rahoton lamarin, a ranar Talata 6 ga watan Fabrairun 2024, rundunar ta kai samame maɓoyar ’yan ta’addan da ke yankin Adeke, inda ta kamo wadanda ake zargin.
Ya kara da cewa a ranar Asabar 24 ga wata da dare sun cafke wasu mutane biyu a anguwar Adoka, a wani sammen haɗin guiwa da ’yan sa-kai a wani wuri da ’yan fashin ke yi wa mutane kwanton bauna.
Kwamishinan ya bayyana cewa sun kwace bindigogi da kuma katinan cirar kuɗi da dama a hannun ’yan fashin.
Ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin domin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.