An kama ’yan fashi 26 an ƙwato wayoyin sata 126 a Kano
Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Kano ta kwato wayoyin sata 126ntate da kama masu fashin waya 26.
Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Kano ta kwato wayoyin sata 126ntate da kama masu fashin waya 26.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kuma ƙwato miyagun ƙwayoyi da makamai da kwamfutocin laptop a hannun ’yan fashin.
Ya ce an kama ’yan fashin ne a kwanaki 12 na farkon watan nan na Satumba, 2024.
Ya ce an gudanar da aikin ne domin kakkaɓe ’yan fashin waya da dangoginsu da suka addabi al’ummar birnin Kano.
- Yaron gida ya shiga hannu kan yin luwaɗi da jikokin uban gidansa
- Hadimin Gwamnan Kano ya sauya sheƙa zuwa APC
Kiyawa ya ce za a gurfanar da waɗanda aka kaman a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka.
Wayoyin da sauran kayan satan kuma za a mayar wa masu su bayan an tantance su.