An kama ’yan kasashen waje da kokon kan mutum a Ogun

Dukkansu dai wannan ba shi ne karon farko da suke tono gawarwaki don yin tsafin ba.

An kama ’yan kasashen waje da kokon kan mutum a Ogun

Matsafan da aka kama da kokon kan mutum a Ogun

Jami’an ’yan sanda a Jihar Ogun sun bajelolin wasu mutum biyu ’yan kasashen waje wadanda aka kama da kokon kan mutum.

An dai gabatar da mutanen ne, Monday Karezu mai kimanin shekara 32 da kuma Anagonou Kamelan mai shekara 44, a hedkwatar rundunar da ke Abeokuta ranar Lahadi.

Kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi, ya ce daya daga cikin mutanen dan kasar Togo ne, dayan kuma dan Jamhuriyar Benin.

Ya ce jami’an Sashen Manyan Laifuka na rundunar ne suka cafke mutanen bayan samun wasu rahotannin sirri cewa suna kan hanyar zuwa wajen wani matsafin don yin tsafin samun kudi

A cewar Abimbola, bayan samun bayanan ne, DSP Nurudeen Gafar ya jagoranci ayarin jami’an zuwa gidan matsafin inda suka yi masa kwanton bauna.

Ya ce bayan kimanin sa’a biyu, sai wadanda ake zargin suka isa wajen akan babur da wata leda da ke dauke da kan mutum din.

Kakakin ’yan sandan ya ce binciken da aka yi ya gano cewa kan na wata mata ne da ta mutu wata uku da suka gabata sakamakon haihuwa, kuma aka binneta a wani waje da ke kusa da unguwar Sabo a birnin Abeokuta.

Abimbola ya kuma ce dan Jamhuriyar Benin din ya taba kashe ’yar cikinsa mai wata tara da haihuwa ya kuma yi amfani da kan nata domin tsafi, amma bukatarsa ba ta biya ba.

Bugu da kari, Monday ma ya taba tono wata gawar, ya cire kanta domin tsafin amma shima hakarsa ta gaza cimma ruwa.