An kama ’yan kunar bakin wake 2 a Borno

Sojoji sun kama ’yan kunar bakin waken bayan sanya dokar hana zirga-zirga a yankunan Gwoza da Pulka

An kama ’yan kunar bakin wake 2 a Borno

Gwamantin Jihar Borno ta sanar da kama ’yan kubar bakin wake biyu a Karamar Hukumar Gwoza.

Sakatariyar karamar hukumar, Hajiya Fatimah Musa, ta ce an kama maharan ne bayan wani harin kunar bakin wake da kungiyar Boko Haram ta kai wurin liyafar daurin aure ranar Asabar.

Ta bayyana cewa an yi nasarar kama ’yan kunar bakin waken ne yankunan Gwoza da Pulka, bayan sojoji sunsanya dokar hana zirga-zirga zirga a yankin, jim kadan bayan harin.

Ta bayyana cewa nasarar da sojojin suka samu zai dawo da zaman lafiya a karamar hukumar.

Ta kuma yi kira ga al’ummar yankin da su ba wa sojojin hadin kai tare da kai rahoton duk wanda ba su yarda da motsinsa ba ga jami’an tsaro.

Sakatariyar karamar hukumar ta ce zuwa yanzu mutun 21 sun rasa rayukansu a sakamakon harin, ciki har da mata da kananan yara, wasu 48 kuma sun samu munanan raunuka.

“An yi jana’izar wadanda suka rasu bisa tsarin Muslunci,” in ji ta.

Tinubu, Atiku, gwamnonin Arewa sun jajanta

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da harin bam din, inda ya ce duk masu hannu a harin za su girbi abin a suka shuka.

Shugaban a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta bar kasar ta shiga cikin “zamanin tsoro, bakin ciki, da zubar da jini ba.”

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron ’yan kasa, don tabbatar da cewa “an kawar da masu kawo cikas ga al’umma da zaman lafiya gaba daya.”

Shi kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kuma yi Allah wadai da harin, yana mai rokon gwamnatin tarayya da kada ta bari yankin Arewa maso Gabas ya koma fagen ta’addanci.

Atiku ya roki gwamnati mai ci da ta ci gaba da sauke nauyin da ke wuyanta, yana mai zargin gwamnatin da rashin tsayin daka wajen tabbatar da dorewar nasarorin da jami’an tsaro suka samu.

Ya ce, “abin bakin ciki ne yadda al’amuran ta’addanci ke sake kunno kai, kuma, hakika, suna tada zaune tsaye a yankin Arewa maso Gabas.”

Ya kuma jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, inda ya ce, “Addu’a ce ta Allah Ya ba wa wadanda suka samu rauni lafiya.

A halin da ake ciki, kungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) ta jajanta wa wadanda abin ya shafa, gwamnati da al’ummar jihar Borno.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi Allah wadai da harin, wanda ya yi sanadin asarar rayuka babu gaira babu dalili, tare da jikkata wasu da dama.

Sanarwar da mai magana da yawunsa Ismaila Uba Misilli ya fitar, ta jaddada cewa irin wannan ta’addanci ba shi da gurbi a cikin al’umma mai zaman lafiya da ci gaba.

Don haka ya yi kira da a hada karfi da karfe a tsakanin al’ummar Arewacin Najeriya wajen yakar ayyukan ta’addanci.

 

Daga: Olatunji Omirin (Maiduguri), Haruna Gimba Yaya (Gombe), Sagir Kano Saleh, Saawua Terzungwe & Baba Martins (Abuja)