An kama ‘yan kungiyar asiri da ke dibar mambobinsu ta Facebook

Rundunar ‘yan sanda a Legas ta kame wani madugun ‘yan kungiyar asiri da ke dibar mambobinsa ta kafar Facebook da sauran kafafan sada zumunta na yanar gizo.  Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana ya shaidawa Aminiya cewa, madugun ‘yan kungiyar mai suna Maliki Bello mai shekaru 22 ya shaida wa […]

An kama ‘yan kungiyar asiri da ke dibar mambobinsu ta Facebook

Maliki Bello Madugun qungiyar asirin Berri Boys

Rundunar ‘yan sanda a Legas ta kame wani madugun ‘yan kungiyar asiri da ke dibar mambobinsa ta kafar Facebook da sauran kafafan sada zumunta na yanar gizo. 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana ya shaidawa Aminiya cewa, madugun ‘yan kungiyar mai suna Maliki Bello mai shekaru 22 ya shaida wa rundunar cewa, an shigar da shi kungiyar asiri ne tun yana dan shekara 12 a lokacin da yake aji daya a makarantar karamar makarantar sakandare.

Inda daga nan ya kai matakin madugun na kungiyar asiri ta ‘Berry Boys’, ya ce, ‘yan kungiyar asirin na kiran madugun nasu da suna ‘Supreme Cult Leader’ a turance, baya ga madugun, jami’anmu sun kame ‘yan kugiyar asirin 11, su ne ‘yan kungiyar asirin da ke addabar shiyoyin unguwannin Idia-arba, Lawanson, Dosunmu, Ashimowo Bakare, Omo-Bola da Mushin, aikace aikacen su ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dama.” In ji shi.

A cewar DSP Bala Elkana, ‘yan kungiyar asirin ta nada shafi a Facebook mai suna ‘Bbl Baloteli’ da ke da manbobi 1,928, ya ce akwai jami’an hukumar ‘yan sandan na musamman da Kwamishinan ‘yan sanda Legas CP Hakeem Odumosu, PSC domin kawar da batagarin da ke tayar da hankulan jama’a.