An kama ‘yan kungiyar asiri dauke da dan kanfai
Dubun wasu ‘yan kungiyar asiri ta cika a daidai lokacin da suke kokarin rantsar da sabbin manbobin kungiyar a daura da garin Shagamu a Jihar Ogun. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa, jami’in ‘yan sanda shiyyar Ogijo CSP Muhammad Sulaiman Baba ne ya sami […]
Dubun wasu ‘yan kungiyar asiri ta cika a daidai lokacin da suke kokarin rantsar da sabbin manbobin kungiyar a daura da garin Shagamu a Jihar Ogun.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa, jami’in ‘yan sanda shiyyar Ogijo CSP Muhammad Sulaiman Baba ne ya sami bayanan sirri game da ‘yan kungiyar asirin wadanda ke shirin rantsar da sabbin manbobin su, “Nan take ya jagoranci wasu jami’an mu da ke aiki a karkashin sa wadanda suka yi wa ‘yan kungiyar asirin kofar rago suka kame mutum 3 a cikin su, an kama su da wukake guda biyu daya daga ciki na dauke da busasshen jini, da dan kanfai na mata wanda aka sanya kayayyakin siddabaru a jikin sa da dai sauran kayayyakin tsafe-tsafe” in ji shi .
Ya ce, wadanda aka kame sun hadar da Olagboye Abidemi mai shekaru 32 da Olasemojo Michael dan shekara 28 sai Wasiu Waheed mai shekaru 23, ya ce, dukkanin su sun amsa laifin su inda suka ce su ‘yan kungiyar asiri ne ta EIYE, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun Bashir Makama, ya bada umarnin tasa keyar wadanda ake zargin zuwa sashin rundunar da ke yaki da ‘yan kungiyar asiri domin zurfafa bincike kafin daga bisani a gabatar da su a gaban kotu, ya ce rundunar ba zata lamunta da miyagun aika-aikar ‘yan kungiyar asiri ba.
Haka zalika rundunar ta kame wani matashi da ake zargi da hallaka abokin sa har lahira bayan da suka yi tatul da barasa a wajen bikin liyafa a ranar 5 ga watan nan, lokacin da musu ya kaure a tsakanin su inda wanda ake zargin mai suna Oni Olohunwa mai shekaru 28 ya daba wa abokin sa wuka a kirji a baya bayan nan lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar abokin nasa mai suna Baraka Taiwo a lokacin da likitoci ke kokarin ceto rayuwar sa.