An kama ’yan luwadi’ a Gombe

Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata luwadi.

An kama ’yan luwadi’ a Gombe

Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta kama matasa biyu da ake zargi da aikata luwadi.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar, ASP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Yulin 2024, rundunar ta samu labarin  cewa an kama wadanda ake zargin suna saduwa da juna ta dubura a unguwar Kanbariki da ke garin Kumo.

Daga nan rundunar ta je wuri ta cafke wadanda ake zargin inda aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

Buhari ya bayyana cewa a lokacin da ake gudanar da bincike wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.

Ya ce daya daga cikinsu ya bayyana cewa dayan ya yi alkawarin ba shi kudi N15,000 idan suka kammala.

Amma bayan ya samu biyan bukatar tasa sai ya nuna masa cewa ba zai ba shi kudin ba.

Jami’in ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike