An kama alhazan Najeriya 7 marasa katin shaida a Makkah
Saudiyya ta ƙirƙiro da katin NUSUK domin tantance maniyyatan da aka bai wa izinin Hajjin na bana.
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ce, an kama wasu ‘yan ƙasar bakwai da ba su da katin shaidarsu ta NUSUK.
Aminiya ta ruwaito cewa, ƙasar Saudiyya ce ta ƙirƙiro da katin NUSUK domin tantance maniyyatan da suka halasta zuwa aikin hajjin 2024.
An dai ƙirƙiro katin ne domin daƙile sake aukuwar lamarin da ya faru a bara inda mahajjata ba bisa ƙa’ida ba suka mamaye sansanonin Mina wanda ya sanya wasu ‘yan Nijeriya ba su samu damar yin hidimar aikin da suka biya ba.
Wata takardar da aka aika wa Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai a Makkah, ta ce an kama maniyyatan ne a gaban otal ɗinsu kuma daga jihohi biyu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “NAHCON na so ta sake nanata shawararta da kira ga alhazai kan karɓar katin shaida na NUSUK da ake yi a ƙasar Saudiyya.
“Hukumar ta yi gargaɗin cewa tuni aka kama wasu alhazan Najeriya bakwai daga jihohi biyu a gaban otal ɗinsu a ranakun 5 da 6 ga watan Yuni, saboda rashin katin shaidar NUSUK.”
Sanarwar ta bayyana cewa wannan gargaɗi yana da muhimmanci saboda hukumomi za su ci gaba da kama mutanen da ba sa tare da katunansu ba.
Don haka an buƙaci dukkan mahukunta da masu ruwa da tsaki da su ƙara wayar da kan alhazansu kan wajibcin mallakar katin shaida na NUSUK wanda dole ne a karɓo idan sun isa Makka daga jami’an Mutawwif.