An kama ’yan Najeriya 9 a farfelan jirgin ruwa za su je Turai

Sojojin ruwan Najeriya sun zakulo wasu matasa tara da suka boye a farfelar wani jirgin ruwa da nufin ya kai su zuwa Turai ba bisa ka’ida ba.

An kama ’yan Najeriya 9 a farfelan jirgin ruwa za su je Turai

Sojojin ruwan Najeriya da ke sintiri sun zakulo wasu matasa tara da suka boye a farfelar wani jirgin ruwa da nufin zuwa Turai ba bisa ka’ida ba.

A ranar Litinin Kwamandan jirgin, Commodore Kolawole Oguntuga, ya sanar cewa an gano mutanen ne a ranar 3 ga watan Fabrairu a yayin da jirgin ruwan ke kokarin barin kasar zuwa kasar Spain.

Oguntuga ya ce mutanen da aka kama matasa maza ne masu shekaru 24 zuwa 36 daga jihohin Delta, Edo, Imo, Ondo, Ekiti da Bayelsa,  sai wani dan shekau 57 daga Delta.

“An gano su da kuma zakulo su abin yabawa ne, domin kuwa, kariya ce daga yiwuwar zamun barazanar tsaro ga jirgin da ma’aikatansa da kuma rayuwarsu a yayin wannan a teku ga jirgin da ma’aikatansa,” kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN)

Oguntuga ya kara da cewa an mika su ga Hukumar Shige-da-fice ta Najeriya (NIS) bisa ka’idojin da aka kafa domin daukar matakin da ya dace.

NAJERIYA A YAU: Turka-Turkar Da Ta Dabaibaye Zaben Jihar Edo

Ambaliya ta shafi mutum miliyan 1.6 a Nijeriya — NEMA

Haɗurra 3 sun yi ajalin mutane 91 a kwanaki takwas — FRSC

Abba zai gina wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa gidaje a Kano