An kama ’yan sanda uku bisa zargin kisan direba

Kwanishinan ’Yan sanda a Jihar Delta, Zanna Ibrahim ya sanar da kama wasu jami’an ’yan sanda ake zargi da laifin kashe direban wata mota mai suna Ejovwokereoghare, a kusa da kauyen Emede na jihar. ’Yan sandan uku suna aiki a runduna ta 33 da ke Ado Ekiti, jihar Ekiti amma Kwamishinan ’yan sandan bai bayyana […]

An kama ’yan sanda uku bisa zargin kisan direba

Kwanishinan ’Yan sanda a Jihar Delta, Zanna Ibrahim ya sanar da kama wasu jami’an ’yan sanda ake zargi da laifin kashe direban wata mota mai suna Ejovwokereoghare, a kusa da kauyen Emede na jihar.

’Yan sandan uku suna aiki a runduna ta 33 da ke Ado Ekiti, jihar Ekiti amma Kwamishinan ’yan sandan bai bayyana wa manema labarai sunayensu ba. Ya ce: “Za a kai su kotu a kan zargin sun yi kisan kai da kuma nuna rashin qwarewar aiki.”

Ya ci gaba da bayanin cewa: “Jami’an suna aikin rakiyar wani Daraktan kamfanin Jonesco ne mai suna Arigbogha Johnny, kan titin filin jirgin sama da ke garin Warri, a lokacin ne suka yi kisan da ake zargin su da aikatawa.”

Ya qara da cewa wata mace da ke gefen hanya mai suna Agwere Hannahta ce ta sanar wa da ofishin ’yan sanda cewa suna tare da wanda aka kashen a gefen hanya sai ’yan sandan suka zo wucewa a wata mota kirar Hilux mai lamba PF 297 SPY, lokacin su kuma sun dawo daga wurin biki qauyen Emeden. Ita dai matar ta samu raunuka sakamakon harbi da aka yi masu yayin da shi kuma harsashi ya yi masa jina-jina, aka kwashe su zuwa babban asibitin Olomoro. Nan ne likitoci suka tabbatar musu da cewa mutumin ya mutu.