An kama ’yan Togo biyu kan shirin garkuwa da mutum

SP Adetoun Ejire Adeyemi ta ce, waɗanda ake zargin sun yi wa wani mazaunin jihar barazanar cewa, za su yi garkuwa da shi tare da kashe ƙaninsa idan bai biya kuɗin ba.

An kama ’yan Togo biyu kan shirin garkuwa da mutum

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta kama wasu ’yan ƙasar Togo biyu bisa zargin shirya garkuwa da wani mutum tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 22.

Kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire Adeyemi ta ce, waɗanda ake zargin sun yi wa wani mazaunin jihar barazanar cewa, za su yi garkuwa da shi tare da kashe ƙaninsa idan bai biya kuɗin ba.

Ta ce, bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaro sun gano tare da kama mutanen biyu, inda suka ƙwato wayar salula da ake zargin an yi amfani da ita wajen yin kiran barazanar.

A cewar rundunar, waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu a lamarin yayin da ake ci gaba da bincike domin cafke sauran waɗanda ake zargin suna cikin tawagar ‘yan bindigar.

An gurfanar da wanda ya kashe matarsa da ƙona gida

Atiku ya caccaki Tinubu kan rikicin BCDA

An kama ’yan Togo biyu kan shirin garkuwa da mutum

’Yan bindiga sun sace ’yan gudun hijira a Sakkwato

Tags