An kama ’yar shekara 20 da buhu 5 na tabar wiwi

Makwabtaka sun fallasa yadda masoyan suke tara tabar wiwi a cikin gidansu

An kama ’yar shekara 20 da buhu 5 na tabar wiwi

An cafke wata budurwa ’yar shekara 20 tare da saurayinta da buhuna biyar na tabar wiwi a Jihar Edo.

’Yan sanda sun cafke budurwar da saurayinta mai shekaru 40 ne a gidan da suke zama a unguwar Ologbo a Karamar Hukumar Ikpoba-Okha.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Edo, Chidi Nwabizor, ya ce, rundunar ta yi nasarar cafke su ne bayan makwabtaka sun kawo rahoton zargin masoyan suna tara ganyen tabar wiwi a cikin gidan.

Bayan an kai samame gidan ne kuma aka gano buhuna biyar na tabar wiwi a ciki .

Jami’in ya ce rundunar ta kuma kama wasu mutane hudu kan zargin fasa wani turken sadarwa na kamfanin Airtel, da sace baturansa da kudinsu ya kai Naira miliyan 12 a garin Benin, babban birnin jihar.

Ya ce an cafke su ne a cikin motarsu bayan sun je shan mai a wani gidan mai, amma da aka bincika motar ba a ga alamar kayan laifi a cikinta ba.

Ya ce wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin, duk da cewa rundunar ta samu kiran neman agaji da ke nuna cewa su ne suka sace batiran.

Don haka ya ce za a ci ca gaba da bincike kan lamarin.