An kama ’yar Sifen da Naira miliyan 11 da dubu 877 a cikinta

Wata mata ’yar akasar Spain da ta fito daga tsibirin Domican, an kamata afilin jirgin saman Punta Cana cuse da kudi a cikinta har Yuro dubu 55 da 500 (daidia da Naira 11,877,000) a cikinta, sannan wasu kudin dubu 54 da 600 a cikin Jakarta, bayan ta dawo daga kasar Belgium a daidai lokacin da […]

An kama ’yar Sifen da Naira miliyan 11 da dubu 877 a cikinta
An kama ’yar Sifen da Naira miliyan 11 da dubu 877 a cikinta

Wata mata ’yar akasar Spain da ta fito daga tsibirin Domican, an kamata afilin jirgin saman Punta Cana cuse da kudi a cikinta har Yuro dubu 55 da 500 (daidia da Naira 11,877,000) a cikinta, sannan wasu kudin dubu 54 da 600 a cikin Jakarta, bayan ta dawo daga kasar Belgium a daidai lokacin da ta shiga hannun ’yan sandan da ke farautar fataken miyagun kwayoyi.

Jami’an asiri sun samu labarin matar, inda aka gargade su game da cewa tana dauke da kudi a cikinta, da wasu jakunkuna 16, kuma da aka dauki hoton cikin ta hanyar d-ray an tabbatar da gaskiyar lamarin. Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ne ya baza labarin wannan mata a duniya.
An dai samu wannan mata dauke da kudin da kimarsu ya kai Dalar Amurka dubu 140, sabanin Dala dubu 10 da aka amince mutum ya yi tafiya da su.