An kama yaro mai shekara 14 a cikin ’yan bindigar Katsina
Yaron ya ce ya kashe mutane kuma ya iya sarrafa bindiga kirar AK 47.
Jami’an tsaro sun kama wani yaro mai shekara 14 a cikin ’yan bindiga da dubunsu ta cika a Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina ta gabatar da yaron ne bayan ’yan banga sun taimaka aka kama shi kan ayyukan ’yan bindiga da satar shanu a yankinsu.
- Matashi yana neman wanda zai saye shi a Kano
- Mahara sun fasa gidan yari sun saki daruruwan fursunoni a Oyo
Yaron wanda dubunsa ta cika a ranar 12 ga watan Oktoba, 2021, ya shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa ya iya sarrafara bindiga kirar AK 47, kuma da shi aka kai wasu hare-haren ’yan bindga a yankinsu da ke Karamar Hukumar Jibia ta Jihar.
Da yake gabatar da yaron da sauran ’yan bindigar da suka shiga hannu, kakakin ’yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya shaida wa ’yan jarida cewa yaron ya amsa cewa ya taba kashe mutum biyu a wani hari da gungunsu ya kai.