An kame Asari Dokubo a Jamhuriyar Benin

Rundunar ’yan sandan kasar jamhuriyar Benin, wadanda ake  kira Jandarma da Faransanci, sun kame tsohon dan fafutikar yankin Neja Delta, Alhaji Mujahid Asari Dokubo a garin Kwatano.Rahotanni sun nuna cewa an kama Mujahid Asari a ranar Talatar da ta gabata ne da misalin karfe daya na rana. Wata sanarwa da lauyansa, Mista Festus Keyamo ya […]

An kame Asari Dokubo a Jamhuriyar Benin

Alhaji Mujahid Asari Dokubo Rundunar ’yan sandan kasar jamhuriyar Benin, wadanda ake  kira Jandarma da Faransanci, sun kame tsohon dan fafutikar yankin Neja Delta, Alhaji Mujahid Asari Dokubo a garin Kwatano.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Mujahid Asari a ranar Talatar da ta gabata ne da misalin karfe daya na rana.
Wata sanarwa da lauyansa, Mista Festus Keyamo ya sanya wa hannu, a Legas ta tabbatar da kamun da ’yan sanda suka yi masa.
Sanarwar ta nuna cewa  an kame Mujahid Asari a daidai shataletalen titin Lubeleyi, inda ’yan sandan suka kai shi wani wuri da ba su bayyana ba.
Lauyan ya yi zargin cewa kamen ba shi da nasaba da wani laifi da ake zargin ya aikata, domin Mujahid Asari ya yi shekaru a kasar Benin yana gudanar da kasuwanci, inda ya mallaki kadarori a da suka hada da wata jami’a da ya bude don bunkasa ilimi a kasar mai suna King Amachree African Unibersity, wacce za ta fara ba da shaidar karatun digiri a shekarar 2014.
Sanarwar ta yi bayani dalla-dalla, inda ta ce ya mallaki gidaje da makarantu da kuma cibiyoyin ilimi a kasar. Jandarmomi sun bincika duk wadannan wurare, amma ba su sami wani abin cutarwa ba.
Sanarwar ta ci ga da cewa, “Muna da tabbacin cewa kamun da aka yi masa wadansu mutane ne suka shirya shi tare da hadin bakin wasu jami’ai na gwamnatin Benin don a tsare shi a can, musamman ma da shekarar 2015 ta ke karatowa. Muna kira ga gwmnatin Nijeriya ta gaggauta shiga tsakani don tabbatar da cewa wani abu bai same shi ba kuma muna bukatar gwamnati ta yi amfani da duk wata hanyar diplomaciya don ganin an gaggauta sako shi ya dawo Najeriya’.