Lahadi ce ranar Sallah, inji Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da ranar Lahadi a matsayin ranar karamar Sallah. Yayin sanar da kammala azumin watan Ramadanan bana, Sarkin Musulmin ya ce ranar Lahadi 24 ga watan Mayu ita ce ranar 1 ga watan Shawwal 1441 bayan Hijira, kuma ranar karamar Sallah. Sarkin Musulmin ya ce an azumci […]

Lahadi ce ranar Sallah, inji Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da ranar Lahadi a matsayin ranar karamar Sallah.

Yayin sanar da kammala azumin watan Ramadanan bana, Sarkin Musulmin ya ce ranar Lahadi 24 ga watan Mayu ita ce ranar 1 ga watan Shawwal 1441 bayan Hijira, kuma ranar karamar Sallah.

Sarkin Musulmin ya ce an azumci kwana 30 a Ramadanan bana ne sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Juma’a 29 ga watan.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren Majalisar kolin harkokin Musulunci ta Najeri, Farfesa Salisu Shehu ya fitar a daren Asabar 23 ga watan Mayu: “Majalisar na rokon Allah Ya karbi azuminmu da dukkan ayyukan kwarai da muka yi a cikin Ramadan, kuma Ya sa mu yi Sallah cikin farin ciki da aminci.

“Muna rokon Allah da rahamarSa, Ya yaye wa Najeriya da sauran kasashen duniya annobar coronavirus”, inji Salisu Shehu.