An kammala babban zaben shekarar 2019 saura cika alkawurra
A ranar Asabar 9-03-2019, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta kawo karshen babban zaben wannan shekarar ta 2019, bayan ta dage zabubbukan da mako daya. Tun farko dai tsarin jadawalin shirye-shiryen babban zaben na bana da hukumar ta INEC, ta fitar kunsan shekara daya da ta gabata wato a shekarar 2018, ya […]
A ranar Asabar 9-03-2019, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta kawo karshen babban zaben wannan shekarar ta 2019, bayan ta dage zabubbukan da mako daya. Tun farko dai tsarin jadawalin shirye-shiryen babban zaben na bana da hukumar ta INEC, ta fitar kunsan shekara daya da ta gabata wato a shekarar 2018, ya tabbatar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa da na `yan Majalisun Dokoki na kasa a ranar 16 ga watan Fabrairun banan, ya yin da za a gudanar da na gwamnoni da na `yan Majalisun Dokoki na jihohi a ranar 2 ga wannan watan na Maris. Amma haka kwatsam ya rage awoyi bakwai da rabi a fara zaben wato da karfe biyu da rabi 2:30am na tsakar daren wayewar garin Asabar din, sai shugaban Hukumar ta INEC na kasa baki daya Farfesa Mahmood Yakubu ya shaida wa manema labarai cewa bisa ga wasu dalilai da su ka sha kan Hukumar, sun dage zaben shugaban kasar da na `yan Majalisun Dokoki na kasa da kwana bakwai, wato zuwa ranar 23 ga watan na Fabrairu. Shi kuma na gwamnoni da `yan Majalisun Dokoki na jihohi ya tashi daga ranar 2 ga wannan watan na Maris zuwa 9 ga watan.
Ga shi zuwa yanzu cikin yardar Allah an kammala zabubbukan a kasa baki daya (akan na shugaban kasa da na `yan Majalisun Dokoki na kasa) da jihohi 29, inda aka yi zaben gwamnomin jihohi, kasancewar a jihohi 7, wato Ekiti da Kogi da Osun da Edo da Anambara da Ondo da Bayelsa, su zabubbukan gwamnoninsu za su dau lokuta daban-daban daga nan har shekarar 2022, in Allah Ya kai rai. Mai karatu kar ka manta a jihohin Kano da Binuwai da Filato da Sakkwato da Adamawa da Bauchi har zuwa wannan lokaci ba a kammala zabubbukan gwamnonin jihohinsu ba, bisa ga abinda Hukamar zabe ta INEC, ta kira, ba a karkare shi ba. A jihar Ribas kuwa kwata-kwata Hukumar ta INEC ta fadi ba ta samu sukunin gudanar da zabubbukan gwamna da na `yan Majalisar Dokokin jihar, bisa ga abin da ta kira tashe-tashen hankula da aka rinka samu da ma barazana akan rayukan ma`aikatanta, a ranar 9 ga wannan watan, don haka sai nan gaba shi ma.
Kodayake kungiyoyin kasa da kasa irin na kungiyar Tarayyar Turai wato EU da Kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma da ma na cikin gida da su ka sa ido a zabubbukan sun yaba akan irin yadda aka gudanar da zabubbukan cikin kwanciyar hankali da lumana da kamanta gaskiya da adalci gwargwadon zarafi, sabanin zabubbukan baya. Amma kuma sun koka akan irin yadda aka rinka amfani da kudi cikin zabubbuka. Wannan batun yin amfani da kudi a cikin gudanar da zaben kasar nan yana neman ya zame mana wata mummunar annoba, duk kuwa da a kullum ana ta gargadi da nuna kyama akanta, amma a kullum sai daukar wani sabon salo ta ke. Alal misali a wannan karon an yi zargin cewa a jihohi irin su Kano da Jigawa da Katsina da makamantansu ta kai fagen har Naira 50, an ba masu kada kuri`a don su zabi dan takara. An kuma kuma yi zargin cewa akwai inda aka rinka bada abincin da ba ma zai kosar da mai zabe ba, duk dai don ya yi zabe. Allah Ka yi mana maganin wannan rashin kishin kai da ma na kasa da kuma matacciyar zuciya da mutane ke sayar da `yancinsu da na zuriyarsu akan abinda bai taka karaya ya karya ba.
Wata kuma babbar annoba da akai fama da ita a lokacin zabubbukan na bana, wadda duk tafi wadancan da na ambata a sama muni, wadda Allah SWT da Ya haliccemu Ya ke fushi da ita, ita ce irin yadda aka rinka kashe-kashen rayukan al`umma da raunata juna da sunan banbancin ra`ayin siyasa.Tun daga cikin watan Satumba zuwa farko-farkon na Oktoban bara da aka gudanar da zabubbukan fitar da gwanayen da za su tsayawa jam`iyyun takarar zabubbukan banan, akai ta fama da fitintunu da fadace-fadace da sunan siyasa, al`amarin da ya kai aka halaka mutane da dama, baya ga wadanda aka jikkata. Jihohi irinsu hada Zamfara da Kano da Ribas da Legas da Imo na cikin jihohin da akai ta samun waccan balahira.
Saura da me? Babban zaben shekarar 2019, dai cikin yardar Allah ya kusa zuwa karshe in Allah Ya so, wadanda su ka yi nasara sun yi, wadanda su ka fadi sun fadi, sai kuma su ci gaba da shirin na shekarar 2023, in Allah Ya nuna mana. Ga `yan kasa da ma masu mulkin sai mu ci gaba da addu`o`in Allah Ya kama mana baki daya ta yadda zaman lafiya karuwar arziki da kwanciyar hankali za su ci gaba da ingata a kasar mu baki daya. Ina sa ne da cewa duk dan takarar da bai gamsu da yadda aka gudanar da zaben ba yana da `yancin ya kai kara gaban Kotunan bin kadin zabubbukan da aka kafa. Tuni dai dan takarar neman shugabancin kasa na jam`iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da jam`iyyarsa su ka tunkari tokun, don bin kadin yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar. Na san kuma da yawa za su biyo baya, dama haka demokradiyya ta gada inda ba ka gamsu ba da abin da aka yi, sai ka garzaya gaban shari`a, maimakon ka rinka sa ana tada husuma.
A zaman jiran hukunce-hukuncen da kotuna ta yanke, babban abin da ya rage ma shugabannin da ake zabe, shi ne su dukufa wajen ganin sun cikasawa wadanda su ka zabe su alkawurran da su kai masu na ganin sun kyautata rayuwarsu akan samar da tsaro kasancewar batun tsaron, shi ke babbar barazana a rayuwar mutum kasar nan, bisa ga la`akari da ba shiyyar da ba ta fama da wannan annoba. Kama daga rikicin Boko Haram a jihohin shiyyar Arewa maso Gabas zuwa sace da yi garkuwa da mutane don neman kudin fansa a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da wasu jihohi na kudancin kasar nan. Dadin dadawa ana kuma fama da rikice-rikice masu kama da na addini da kabilanci a jihohin Kaduna da Filato da Taraba, baya ga fadan Fulani makiya da Manoma. Ta`addanci irin na fashi da makami da rikici irin na `yan kungiyar gwagwarmayar tabbatar da kasar Biyafara wato MOSOB da na `yan tsagerun Neja Delta da na `yan tsagerun kungiyar Yarbawa ta OPC, duk ba a daina su akai ba, illa dai sun dan lafa ne.
Tuni shugaba Buhari ya sha alwashin zai ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da tsaro da farfado da tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasan kasar nan. `Yan kasa sun zuba ma shi idanu da addu`ar ganin yadda zai tunkari wadannan matsaloli, musamman kwato dukiyoyin da aka yi almubazzaranci da su da sunan an yi aiki, kamar Dalar Amurkan nan biliyan 16, ta wutar lantarki a zamanin gwamnati tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo.
Ga `yan Majalisun Dokoki na kasa da gwamnonin jihohi da `yan Majalisun Dokoki na jihohinsu da duk wani wanda za a nada akan kowane irin mikami, talakawan kasa suna bukatar sadaukarwarsu, ta yadda za su yi aiki tukuru cikin kamanta gaskiya da adalci cikin tafiyar da amanar wakilcinsu. Talakawa fa na cikin wahala.