An kammala cinikin Mason Mount tsakanin Chelsea da Manchester United

Chelsea ba ta so rabuwa da Mount ba, amma ta gaza wajen cimma yarjejeniya da shi a kan sabon kwantaragi.

An kammala cinikin Mason Mount tsakanin Chelsea da Manchester United

Manchester United ta amince da biyan fam miliyan 55 a kan dan wasan tsakiya na Chelsea, Mason Mount a kan kwantaragin shekaru biyar.

Mount, mai shekaru 24, zai kasance dan wasa na farko da mai horar da ’yan wasan Man U, Erik ten Hag zai sayo a wannan lokaci, a yayin da yake kokarin karfafa tawagarsa don tunkarar gasar Kofin Zakarun nahiyar Turai.

Chelsea ta kashe fam miliyan 600 wajen sayen ’yan wasa a kakar da ta gabata kuma tana bukatar sayar da wasu kafin karshen wannan rana ta 30 ga watan Yuni saboda kada ta samu matsala da dokar takaita kashe kudi wajen cefano ’yan wasa.

Rahotanni su ne Chelsea ba ta so rabuwa da Mount ba, amma ta gaza wajen cimma yarjejeniya da shi a kan sabon kwantaragi, kuma ga shi kwantaraginsa na yanzu zai kare a shekara mai zuwa.

Mount, wanda ya ci kwallaye 33 daga wasanni 195 tun da ya fara yi wa Chelsea wasa a shekarar 2019, ya fuskanci matsalar rauni a kusan karshen kakar da ta gabata, inda Chelsea ta gama a matsayi na 12, kaka mafi muni a gare ta a cikin shekaru 25.

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu