An kammala gasar tseren dawakai ta farko a Masarautar Jama’a
An yi kira ga matasa da su rungumi wasannin gargajiya domin kare al’adu da ƙarfafa haɗin kan al’umma.
An kammala gasar tseren dawakai ta farko da aka shirya a Masarautar Jama’a da ke Jihar Kaduna, inda dokin Magajin Gari ya zama zakara, yayin da na Barade da na Hon. Isiyaka Abdu Ladan suka zo na biyu da na uku.
Dawakai 16 ne suka fafata a gasar da aka gudanar a harabar Fadar Sarkin Jama’a da ke Kafanchan, a gaban ɗimbin masu kallo daga sassa daban-daban.
Da yake jawabi, Mai Martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu II, ta bakin Ciroman Jama’a, Alhaji Kabiru Tanko, ya yaba da yadda aka gudanar da gasar cikin tsari da lumana.
Ya kuma buƙaci al’umma su ci gaba da tallafa wa irin waɗannan shirye-shirye domin bunƙasa al’adun gargajiya da kuma haɓaka harkar tseren dawaki.
Shugaban kwamitin shirya gasar, Danmadamin Jama’a, Alhaji Aminu Isa Muhammadu, ya gode wa mahalarta gasar da jami’an tsaro da kuma al’ummar da suka ba da haɗin kai wajen tabbatar da nasarar shirin.
Shi ma wanda ya shirya gasar, Gado da Masun Jama’a, Alhaji Ibrahim Alake Ahmadu, ya yaba wa masu hannu da shuni da suka tallafa wa gasar da kyaututtuka.
A ƙarshen gasar, an bai wa zakara keken hawa, yayin da waɗanda suka zo na biyu da na uku aka ɗauki nauyin biyan kuɗin karatunsu na shekara guda.
Da suke zantawa da Aminiya, zakarun gasar sun bayyana farin cikinsu, tare da cewa nasarar za ta ƙara musu ƙwarin gwiwar ci gaba da shiga irin waɗannan gasa.
Sun kuma yi kira ga matasa da su rungumi wasannin gargajiya domin kare al’adu da ƙarfafa haɗin kan al’umma.
