An kammala musayar fursunoni a Yemen
A jiya Alhamis ne dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da ’yan tawayen kasar suka kammala musayar daruruwan fursunoni a tsakaninsu.Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da bangarorin biyu suka amince da yarjejeniyar tsagaita bude-wuta yayin da tattaunawar zaman lafiya a tsakaninsu da Majalisar dinkin Duniya ke jagoranta a kasar Switzerland ta shiga […]
A jiya Alhamis ne dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da ’yan tawayen kasar suka kammala musayar daruruwan fursunoni a tsakaninsu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da bangarorin biyu suka amince da yarjejeniyar tsagaita bude-wuta yayin da tattaunawar zaman lafiya a tsakaninsu da Majalisar dinkin Duniya ke jagoranta a kasar Switzerland ta shiga rana ta uku.
Wani mamba a kwamitin kula da fursunoni a kasar Yemen, Mukhtar al-Rabbash ya bayyana cewa sun yi nasarar kammala shirin musayar fursunonin, inda aka yi musayar ’yan tawayen Houthi 370 da dakarun da ke goyon bayan gwamnatin 285.
Rahotanni sun ce, an aiwatar da musayar ce a garin Yafaa a Kudancin Lardin Lahj, kusa da kan iyakar Lardin Bayda.
Sai dai kungiyar Agaji ta Red Cross da ke birnin Sana’a, wadda a baya aka taba sanya ta cikin shirin musayar fursunonin, ta ce ba ta da masaniya game da wannan musayar.
Kamar yadda Majalisar dinkin Duniya ta bayyana, fiye da mutum 5,800 ne rikicin Yemen ya yi sanadiyyar mutuwarsu kuma akasarinsu fararen hula ne, yayin da kimanin dubu 27, suka jikkata daga watan Maris din bana zuwa yanzu.