An kammala rubuta littafin tarihin fitattun ’yan Kano 24
Wani marubuci a Kano, Kabiru Ahmad Ƙwalli, ya ce ya kammala rubuta wani littafi mai suna Mu San Magabata wanda ya ƙunshi tarihin fitattun mutane 24
0-4160×3120-0-0#
Wani marubuci a Kano, Kabiru Ahmad Ƙwalli, ya ce ya kammala rubuta wani littafi mai suna Mu San Magabata wanda ya ƙunshi tarihin fitattun mutane 24 da suka bayar da gudummawa kan ci gaban jihar.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai ranar Alhamis a Kano lokacin ƙaddamar da kwamitin da aka ɗora wa alhakin shirya ƙaddamar da littafin, marubucin ya ce galibin mutanen ba a taɓa rubuta tarihinsu a cikin littafi ba duk da irin tasirin da suka yi a Kano da ma kasa baki daya.
Ya ce mutanen da littafin da bayar da tarihin nasu sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al’umma a fannonin ilimi, shugabanci, kasuwanci da kuma al’adu.
Kabiru Ƙwalli ya kuma ce tunanin rubuta tarihin wadannan manyan mutane ya samo asali ne daga sha’awar ganin ba a bar gudummawar da suka bayar ta shuɗe ba tare da an rubuta ta ba.
Ya ce ba kawai shaharar waɗannan mutane ce ta ja hankalinsa ba, illa irin gudummawar da suka bayar wajen ci gaban ƙasa a rayuwarsu.
Daga cikin mutanen da littafin ya ƙunshi tarihin nasu sun haɗa da Madakin Kano Shehu Ahmad, Alƙalin Kano Umaru, Sheikh Sani Auwalu Darma, Malam Nura Alƙali, Malam Adamu Aminu da kuma Alhaji Uba Ringim.
Sauran sun haɗa da Alhaji Imam Wali, Alhaji Ado Ɗandolo, Kansila Malam Ahmadu Rufa’i Daura, Alhaji Barau Maiwake, Alhaji Baballe Ila, Alhaji Baffa Yola, Alhaji Muhammadu Yankwashi Kazaure, Alhaji Mahe Bashir Wali, Alhaji Salisu Sambajo da Alƙali Husaini Sufi da dai sauransu.
Ya ce an kafa kwamitin kaddamar da littafin ƙarƙashin jagorancin Farfesa Bashir Yusuf tare da mataimakansa Alhaji Ibrahim Aminu Dan’lya da Alhaji Ali Adamu, yayin da Abubakar Farouk Kabara ya kasance sakataren kwamitin.
Marubucin ya bayyana godiyarsa ga kwamitin bisa amincewa da nauyin da suka ɗauka, tare da fatan Allah ya saka musu da alheri.
Kabiru Ahmad Kwalli ya ce littafin zai zama matakin farko na jerin rubuce-rubuce da zai ci gaba da yi kan malamai, sarakuna, attajirai da jajirtattun mata domin tabbatar da tarihin su ya kasance abin koyi ga al’umma.