An kara ceto matashi da iyayensa suka kulle shi shekara 15 a Kano
Karo na biyu ke nan ana kubutar da matasa da iyayensu suka kulle na tsawon shekaru a gida
‘Yan sanda sun gano wani matashi mai shekaru 35 da iyayensa suka kulle shi a daki na tsawon shekara 15 ba tare da yana samun isasshiyar iska ba.
‘Yan sandan da suka kubutar da Ibrahim Lawal a unguwar Sheka, sun garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH)).
Wakilimu ya ce mahaifin matashin, Malam Lawal Sheka wanda aka ce limamin wani masallacin Juma’a ne ya tsere tun bayan samun labarin ‘yan sanda sun kubutar da dan nasa.
Zuwa yanzu mahaifin matashin da ake zargi da kulle dansa tsawon lokacin bai ce uffan game da dalilinsa na yin hakan ba.
Jami’an rundunar’ yan sandan da ke aiki a shiyar karamar Hukumar Kumbotso a karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Habu Ahmad Sani da kuma Baturen ‘Yan Sandan yankin ne suka kai wa matashin dauki.
Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan ‘yan sanda a jihar ta Kano sun gano wani matashi Ahmad Aminu mai shekara 32 da iyayensa suka kulle a daki na shekara bakwai.
Ana zargin mahaifin matashin da kishiyar mahaifiyarsa da kulle shi saboda zargin yana shan kwaya.
A karshen makon jiya a jihar Kebbi ‘yan sanda sun kubutar da wani yaro dan shekara 10 da mahaifinsa da matansa uku suka daure shi shekara biyu a cikin dabbobi, bisa hujjar cewa yana da tabin hankali.