‘An kara ceto wata dalibar Chibok’
Rundunar Sojojin Kasa ta ce an kara ceto wata dalibar makarantar sakandaren garin Chibok, Serah Luka, jiya Alhamis, kwana biyu bayan gano dalibar farko, Amina Aliyu Nkeki. Kakakin rundunar sojin Kanar Sani Kuka Sheka ne ya sanar labarin ceto dalibar ta biyu a daren jiya. Har ila yau, ya ce an kubutar da wadansu mata […]

Rundunar Sojojin Kasa ta ce an kara ceto wata dalibar makarantar sakandaren garin Chibok, Serah Luka, jiya Alhamis, kwana biyu bayan gano dalibar farko, Amina Aliyu Nkeki.
Kakakin rundunar sojin Kanar Sani Kuka Sheka ne ya sanar labarin ceto dalibar ta biyu a daren jiya. Har ila yau, ya ce an kubutar da wadansu mata guda 97 da wasu yara daga hannun ‘yan Boko Haram.
Sai dai wani mai magana da yawun iyayen matan Chibok da aka sace, Yakubu Nkeki, ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa ba ‘yar su ba ce sojojin Najeriya suka ceto.
“Mun bincika sunaye da hotunan yaran da aka sace, sannan mun tuntubi dukkan mutanen da aka sace musu ‘ya’ya, amma sun tabbatar mana cewa yarinyar ba ‘yar su ba ce. Bayanan da muke da su sun tabbatar mana cewa yarinyar da aka gano ranar Alhamis ‘yar wani Fasto ce aka sace ta daga Madagali a Jihar Adamawa,” inji Yakubu.