An kara kudin kujerar Hajji da $250
Hukumar Aikin Hajji ta ce za ta tabbatar maniyyata ba su biya karin Dala 250 da aka samu ba
Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cewa kamfanonin jiragen sama na cikin gida sun bukaci karin Dala 250 a kan kudin tikitin jirgi ga maniyyatan Najeriya.
Shugaban hukumar, Hassan Zikrullah ya bayyana cewa duk da karin da aka samu sakamakon yakin kasar Sudan da ya kara tsawon tafiyar, NAHCON na kokarin ganin maniyyata ba su biya daga aljihunsu ba.
- Yakin Sudan: Sojoji da ’yan tawaye za su koma teburin sulhu a Saudiyya
- Rikicin Sudan: Abu 7 da aka cimma yarjejeniya a kansu
Zikrullah ya bayyana haka ne lokacin da yake sanar da cewa duk da yakin na Sudan, kamfanonin jirgin sama na cikin da aka ba wa jigilar maniyyatan Najeriya sun amince za su yi aikin.
A cewarsa, kamfanonin — Azman, Max Air, Aero Contactors da kuma Air Peace — sun kuma amince da karin Dala 250 a kan kudin kujerar da aka biya da farko.
Ya kara da cewa duk da cewa NAHCON ba ta yanke shawara kan bukatar ba, amma za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin ba maniyyata ne zu su biya karin da aka samu daga aljihunsu ba.
Zikrullah wanda ya yi bayani a ranar Asabar ya ce a ranar 25 ga watan Mayu da muke ciki jirgin farko na maniyyatan Najeriya zuwa zai fara tashi zuwa Kasas Mai Tsarki.
Idan ba manta ba, a kwanakin baya kamfanonin jirage na cikin gida sun bukaci NAHCON ta yi musu karin kudin jigilar alhazai saboda yakin da ya barke a kasar Sudan ya kara nisan tafiyar.
Hakan, sun bayyana cewa zai bukaci karin kudin man jirgi saboda karin sa’o’in da aka samu, akwai kuma karin kudi ga kasashen da yanzu jiragen su za bi ta sararin samaniyarsu.