An kara ranakun fita a jihar Ogun
Za a rika walwala a ranaku biyar a yi kullen kwana biyu a jihar.
Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, ya sauya salon dokar kulle a jihar.
Dapo Abiodun ya takaita dokar kullen zuwa ranaku Asabar da Lahadi maimakon ranaku hudu da ake kullen a baya.
A jawabinsa kai tsaye ga jama’ar jihar ranar Alhamis, gwamnan ya ce za a ba al’ummar jihar damar fita su yi walwala a ranakun Litinin zuwa juma’a daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare.
- An sake tsawaita dokar kulle a Ogun
- An bullo da sabuwar hanyar gwajin Coronavirus a Ogun
- Asirin Masana’antar Jarirai a Ogun ya tuno
Ranakun Asabar da Lahadi kuma za su ci gaba da kasancewa ranakun kulle a jihar.
A baya dai ana bai wa jama’ar jihar damar fita suyi walwala ne a ranakun Litinin, da Laraba da kuma ranar Juma’a.