An kara wa sojoji dubu 10 da ke yaki da Boko Haram girma

Kwamandan Birged na Uku na Sojin Najeriya da ke Damaturu, Birgediya Janar Muhammad Sani Aliyu ya ce kimanin sojoji dubu 10 da ke yaki da ’yan Boko Haram ne aka yi musu karin girma, daga lokacin da aka samu canje-canjen shugabancin dakarun sojin kasar nan.Birgediya Sani Aliyu ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da […]

An kara wa sojoji dubu 10 da ke yaki da Boko Haram girma
An kara wa sojoji dubu 10 da ke yaki da Boko Haram girma

Kwamandan Birged na Uku na Sojin Najeriya da ke Damaturu, Birgediya Janar Muhammad Sani Aliyu ya ce kimanin sojoji dubu 10 da ke yaki da ’yan Boko Haram ne aka yi musu karin girma, daga lokacin da aka samu canje-canjen shugabancin dakarun sojin kasar nan.
Birgediya Sani Aliyu ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da manema labarai a masaukin Shugaban kasa da ke Damaturu, inda ya ce karin girman da aka yi wa sojojin an yi ne don kwazon da suke nunawa a aikin ceto kasa da aka tura su.
Ya kara da cewa, ya hakkake wannan karin girma zai karfafa gwiwa ga dakarun wajen kara kaimi a fagen fama, yayin da sauran ’yan uwansu za su tashi haikan ga yin aiki tukuru don su ma a yi musu karin girma a nan gaba.
Kwamandan ya ce zuwa yanzu sojojin sun karya lagon mayakan Boko Haram, inda suke bin su duk maboyar da suke tare da zakulo su a dazuzzukan Sambisa da Alagarno da Ajigin suna murkushe su da kwato dubban makamai da ceto dimbin mutanen da suke garkuwa da ss.
Ya nemi al’ummomin jihohin Arewa maso Gabas shida da ke karkashin rundunarsa su kara kokari kan goyon bayan da suke ba su a yakin da suke yi da ’yan ta’adda domin da goyon bayan da suke samu ne daga al’umma suke cin galaba a  kan ’yan ta’addan wadanda suke sajewa a cikin jama’a suna aikata ta’asa.
Kwamandan ya ce a makon jiya sojoji sun hallaka ’yan Boko Haram 14 tare da kwato dimbin makamai da suka hada da bindigogi kira AK47 da alburusai da bindiga mai jigidar harsashi da kananan bindigogi da bama-bamai a fafatawar da suka yi a kauyen Chirokusko a hanyar Babbangida.
A wani labarin kuma ’yan ta’addan da ake ji na Boko Haram ne sun kai hari a garin Babbangida da ke karamar Hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe inda suka kashe mutum daya a ranar Asabar da ta gabata.
Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin ne cikin dare a motoci kirar Toyota Hilud guda biyar da babura da dama suna kabbara suna harbe-harbe.
Ya ce an shafe awa uku ana fafatawa a tsakanin maharan da sojoji, inda wajen karfe 4.40 na asuba kura ta lafa.
Birgediya Janar Sani Aliyu ya tabbatar da kai harin inda ya ce sojoji sun kori maharan ba tare da ko jami’insu daya ya jikkata ba.
Ya ce maharan sun tsere da motoci biyu na ’yan sanda tare da kone wani bangare na ofishin ’yan sanda da wasu shaguna biyu da wata cibiyar kamfanin sadarwa.