An tsawaita dokar zaman kulle a Kano
Gwamnatin Kano ta tsawaita wa’adin dokar zaman kulle a jihar da mako guda. A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kwamishinan yada labaran jihar, Malam Muhammad Garba, ya ce an yi karin wa’adin ne bayan tattaunawar da ta dace da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki. A cewar shi manufar tsawaita dokar […]
Gwamnatin Kano ta tsawaita wa’adin dokar zaman kulle a jihar da mako guda.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kwamishinan yada labaran jihar, Malam Muhammad Garba, ya ce an yi karin wa’adin ne bayan tattaunawar da ta dace da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki.
A cewar shi manufar tsawaita dokar ita ce rage yaduwar cutar daga mutum zuwa mutum, hanyar da take saurin yaduwa a tsakanin al’umma.
Sanarwar ta kuma yi kir ga al’umma da su ci gaba da daukar matakan tsafta ta hanyar wanje hannu a kai a kai da amfani da takunkumin rufe fuska, da kuma yin nesa da juna.
Shugaba muhammadu Buhari ne dai ya ayyana dokar hana fita a fadin jihar yayin wani jawabi da ya yi ga al’ummar kasar a watan jiya.