An kara wa’adin hade layin waya da lambar NIN zuwa karshen 2021

Kawo yanzu an yi wa mutum miliyan 66 rajistar lambar NIN.

An kara wa’adin hade layin waya da lambar NIN zuwa karshen 2021

Katin Shaidar Zama Dan Kasa

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita wa’adin da ta sanya na hade lambobin waya da lambar shaidar dan kasa ta NIN zuwar ranar 31 ga watan Disamba, 2021

Hukumar Sadawar ta Kasa (NCC) ta sanar da karin wa’adin, wanda shi ne karo na bakwai, gami da cewa kawo yanzu an yi wa ’yan Najeriya miliyan 66 rajistar lambar NIN.

“Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami ya sanar da amincewar Gwamnatin Tarayya a tsawaita rajistar layukan SIM da kuma hade su da lambar NIN.

“Ana kira ga ’yan kasa na gari da halastattun baki da su tabbata sun yi rajista kafin karshen shekarar 2021,” inji sanarwar da kakakin NCC, Ikechukwu Adinde da takwaransa na hukumar kula da shaidar dan kasa (NIMC), Kayode Adegoke suka fitar.

Sanarwar ta ce an kara wa’adin ne bayan rokon da kamfanonin sadarwa da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren suka yi domin karin ’yan Najeriya su samu.

Sanarwar ta ce kawo yanzu akwai cibiyoyin yin rajistar guda 8,000 a fadin Najeriya.