An kara wa’adin rijistar jarrabawar NECO ta 2018 SSCE
Hukumar kammala jarrabawar sakandare wato NECO ta sanar da kara wa’adin fara rijistar jarrabawar da za a yi watan Nuwamba zuwa Disamba don samun shaidar kammala karatun sakandare (SSCE). Rijistara mai rikon kwarya na Hukumar NECO Mista Abubakar Gana ne ya sanar da hakan yau Talata a Abuja. Gana ya ce, masu son yin jarrabawar […]
Hukumar kammala jarrabawar sakandare wato NECO ta sanar da kara wa’adin fara rijistar jarrabawar da za a yi watan Nuwamba zuwa Disamba don samun shaidar kammala karatun sakandare (SSCE).
Rijistara mai rikon kwarya na Hukumar NECO Mista Abubakar Gana ne ya sanar da hakan yau Talata a Abuja.
Gana ya ce, masu son yin jarrabawar zasu iya yin rijista kai tsaye. Kara wa’adin yana da muhimmanci sakamakon cewa, wasu mason yin jarrabawar basu samu damar yin rijista ba har lokacin wa’adin ranar 17 ga Nuwamba ya cika.