An kara watsar da ’yan Najeriya a saharar Sudan-Masar —Iyaye
Iyayen rukunin farko na daliban Najeriya da aka kwashe daga Sudan sun ce koka cewa yanzu kwana uku amma ’ya’yan nasu ba su shiga kasar Masar ba.
Iyayen daliban Najeriya da aka kwashe a Sudan zuwa kasar Masar sun ce direbobi sun kara watsar da su a cikin sahara bisa umarnin kamfanin jigilar da ya kwaso su.
Iyayen rukunin farko na daliban da suka bar birnin Khartoum na Sudan a ranar Laraba sun koka cewa yanzu kwana uku amma har yanzu ’ya’yan nasu ba su shiga kasar Masar ba.
Sarautar Kano: Dawo da Sanusi II yana hannun Abba —Kwankwaso
Kazamin fada ya barke kusa da Fadar Shugaban Kasar Sudan
Sun bayyana cewa a cikin ayarin har da iyalai da kananan ’ya’yan ’yan Najeriya mazauna Sudan, amma babu wani tanadi da aka yi musu na abinci ko ruwa ko wurin fakewa, a tafiyar ta awa 18 daga Khartoum zuwa iyakar kasar Masar.
Wani daga cikin iyayen da ya ce ’ya’yansa biyu na daga cikin ayarin farko na motocin da suka dauko ’yan Najeriya daga Khartoum ya ce karo na biyu ke nan da kamfanin jigilar yake watsar da ’ya’yan nasu a tsakiyar sahara, a iyakar Sudan da Masar.
Dambarwar kwashe ’yan Najeriya daga Sudan
A ranar Asabar karin motoci 18 dauke da ’yan Najeriya suka kama hanyar zuwa kasar Masar daga Jami’ar Kasa da Kasa ta Afirka da ke birnin Khartoum.
Daga baya ake sa ran rukuni na biyu na wasu motocin za su biyo bayanzu daga hanya daga jami’ar Al-Razi da ke birnin.
Batun kwashe ’yan Najeriya bayan barkewar yaki a Sudan dai ya kasance mai cike da rudani.
Bayan barkewar yakin a ranar 14 ga watan Afrilu daliban Najeriya ke neman a kwashe su daga Sudan kamar yadda sauran kasashe suka yi, inda suke korafin kan abin da suka kira jan kafar gwamnatin Najeriya.
Wasu daga cikinsu dai sun nema wa kansu mafita inda suka bi ta iyakar kasar Habasha suka fice daga Sudan. Akwai wasu kuma da jirgin ruwan kasar Saudiyya ya kwashe tare da ’yan wasu kasashe 74 zuwa Saudiyya.
Daga baya ma’aikatar harkokin waje ta hannun ofishin jakadancin Najeriya da hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) suka ba da sanarwar fara kwashe ’yan Najeriya zuwa kasahe makwabtan Sudan kafin dawowa da su gida.
Ma’aikatar ta bayyana cewa dauko ’yan Najeriya daga Sudan ba zai yiwu ba, saboda yakin ya sa an rufe sararin samaniyar kasar.
A ranar Laraba aka fara kwashe ’yan Najeriya zuwa kasar Masar, daga jami’o’i biyu da ke Khartoum, wadanda ofishin jakadancin ya bukaci ’yan Najeriyar su taru.
Sai dai kuma murna ta koma ciki a ranar Alhamis, inda ana cikin tafiya direbobin motocin suka watsar da su a cikin daji, bisa hujjar rashin cika wa kamfaninsu kudin hayar da aka dauke su.
Daga baya Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje ta sanar cewa an sasanta da kamfanin, za a ci gaba da tafiyar.
A ranar Alhamis din, ragowar ’yan Najeriya da ke Khartoum suka yi korafin cewa ragowar motocin da za su kwashe su ba su zo ba.
A bayaninta, ofishin jakadancin ya nuna bisa alama kamfanin ya dakatar da aiki ne bayan karewar kafin alkalami na kashe 30 na kudin aikin da aka ba shi.
A ranar Juma’a dalibai sun zargi jami’an ofishin jakadancin kasar da ke Sudan da tserewa zuwa Masar su bar su.
Daliban sun kuma koka cewa gwamnatin Najeriya ta ki ba da cikon kudin shi ya sa motocin suka ki daukar su, duk da cewa motocin sun zo.
Amma daga baya ofishin jakadancin ya fitar da sanarwar ci gaba da kwashe ’yan Najeriyan a ranar Asabar kuma akalla motoci 18 dauke da ’yan Najeriya sun bar birnin Khartoum da su.