An karbo daga Abdan ya ce:
335. An karbo daga Abdan ya ce: “Yazid dan Zurai’u ya ba mu labari ya ce, Habib Mu’allimi ya ba mu labari daga Adda’u daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: Lokacin da Annabi (SAW) ya komo daga Hajjinsa ya ce, wa Ummu Sinan mutumiyar Madina: Me ya hana miki Hajji tare […]
335. An karbo daga Abdan ya ce: “Yazid dan Zurai’u ya ba mu labari ya ce, Habib Mu’allimi ya ba mu labari daga Adda’u daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: Lokacin da Annabi (SAW) ya komo daga Hajjinsa ya ce, wa Ummu Sinan mutumiyar Madina: Me ya hana miki Hajji tare da mu? Sai ta ce, “Baban wane (mijina) ya kasance na da rakuma biyu na hawa da ban ruwan gonarmu.” Sai (Annabi) ya ce: “Lallai yin Umara a cikin Ramadan yana daidai da Hajji tare da ni.” dan Juraij ya ruwaito shi daga Adda’u ya ce, “Na ji dan Abbas (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW). Ubaidullahi ya ce, Abdulkarim ya ce, daga Adda’u daga Jabir daga Annabi (SAW).
336. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Abdul Malik dan Umair daga kaza’ata bawan Ziyad ya ce: “Na ji Abu Sa’id yana cewa, “Lallai ya yi yaki tare da Annabi (SAW) har yake-yake goma sha biyu ya ce: “Abubuwa hudu na ji su daga Manzon Allah (SAW) yana ba da labarinsu, sai ya karbe shi daga Annabi (SAW) saboda sun ba ni sha’awa kuma sun shafi mulkina. (1) Kada mace ta yi tafiyar yini biyu ba tare da muharraminta ba. (2) Babu azumin ranaku biyu yinin Idin Layya da Idin Fiir. (3) Babu Sallah bayan salloli biyu, bayan La’asar sai rana ta buya da bayan sallar Asuba har sai rana ta bullo. (4) Ba a kumsa kayan tafiya domin ziyarta wani wurin ibada face Masallatai uku: Masallacin Harami; Masallacina (Madina) da Masallacin Aksa (kudus).”
Babi na Ashirin da Shida:
Wanda ya yi alwashin tafiya zuwa Masallacin Ka’aba:
337. An karbo daga dan Sallam ya ce: “Alfazzariyu ya ba mu labari daga Humaid Addawili ya ce, “Sabit ya ba ni labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ga wani tsoho ana dauke da shi a tsakanin ’ya’yansa biyu. Sai (Annabi) ya ce, “Me ya samu wannan? Suka ce, “Ya yi alwashin tafiya ne zuwa (Ka’aba)? (Annabi) ya ce, “Hakika (Allah) Mawadaci ne game da azabtarwar da wannan yake yi wa kansa. Sai ya umarci da ya hau abin hawa (bai hana masa cika alwashinsa ba).”
338. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Hisham dan Yusuf ya ba mu labari cewa, “Lallai dan Juraij ya ba su labari ya ce: “Sa’id dan Abu Ayyub ya ba ni labari cewa, lallai Yazid dan Abu Habib ya ba shi labari cewa: Lallai Abul Khair ya ba shi labari daga Ukba dan Amir ya ce: “’Yar uwata ta yi alwashi za ta tafi zuwa dakin Allah da kafa. Ta umarce ni in nema mata fatawa ga Annabi (SAW) sai na tambaye shi ya ce: “Lallai ta tafi kuma ta hau abin hawa.” Ya ce, “Abul Khair ya kasance bai rabuwa da Ukba.
339. An karbo daga Abu Asim ya ce: “Daga dan Juraij daga Yahya dan Ayyuba daga Yazid daga Abul Khair daga Ukba sai ya ambaci Hadisin.”
Da Sunan Allah Mai rahama Mai jin kai.
Fifikon garin Madina a kan sauran garuruwa.
Babi na Farko: Haramin Madina
340. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Sabit danYazid ya ba mu labari ya ce, Asim Abu Abdurrahman Ahwal ya ba mu labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Madina haramun ce da wuri kaza zuwa wuri kaza. Ba a cire itaciyarta, ba a kirkirar bidi’a a cikinta. Wanda ya kirkiri wata bidi’a a cikinta to la’anar Allah tana kansa tare da mala’iku da mutane gaba daya,” (Ba a zaunar da dan bidi’a a cikinta).