An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce:

504. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Zuhair ya ba mu labari ya ce, Humaid ya ba mu labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Abdurrahman dan Awfu ya isa Madina sai Annabi (SAW) ya hada su ’yan uwantaka da Sa’ad dan Rabi’u mutumin Madina, kuma Sa’ad ya kasance mawadaci […]

An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce:
An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce:

504. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Zuhair ya ba mu labari ya ce, Humaid ya ba mu labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Abdurrahman dan Awfu ya isa Madina sai Annabi (SAW) ya hada su ’yan uwantaka da Sa’ad dan Rabi’u mutumin Madina, kuma Sa’ad ya kasance mawadaci ne, sai ya ce da Abdurrahman: “Zan raba dukiyata biyu in ba ka daya, kuma zan aurar maka da daya daga cikin matana. Sai (Abdurrahman) ya ce, “Allah Ya sanya albarka cikin iyalanka da dukiyarka, ku nuna mini hanyar kasuwa.” Ba a dade ba face sai ga shi ya komo da sauran cuku (madara) da mai (wanda ya ci ribar kasuwancinsu), ya zo da shi ga masu masaukinsa, ana nan haka muna zaune kamar yadda Allah Ya so mu zauna, sai ga shi ya zo da hasken kanshi (na kunshin aure). Sai Annabi (SAW) ya ce, masa, “Mene ne wannan? Ya ce, “Ya Manzon Allah! Na auri wata mace ce daga matan Madina.” Ya ce, “Nawa ka biya sadakinta? Ya ce, “Gwargwadon nauyin nawat (dan dabino) na zinari.” Ya ce, “To ka yi walima koda da akuya.”

505. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Ukkaz da Majanat da Zul-Majaz kasuwanni ne a Jahiliyya, lokacin da Musulunci ya zo, sai suka rika zaton za su yi laifi idan suka ci gaba da kasuwanci cikinsu har sai da (Allah) Ya saukar da cewa: “Babu laifi a kanku ku nema daga kyautar Ubangijinku a lokacin ayyukan Hajji.” (k:2:198). dan Abbas ya karantata bisa wannan fassara.

Babi na Uku: Halal bayyane take kuma haram a bayyane take a tsakaninsu akwai abubuwa masu rikitarwa (kama da juna):

506. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “dan Abu Addiyi ya ba ni labari daga dan Aunu daga Sha’abi ya ce, “Na ji Nu’aman dan Bashir (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Na ji Annabi (SAW) ya ce, Aliyu dan Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Uyainat ya ba mu labari daga Abu Farwat daga Sha’abi ya ce, “Na ji Nu’aman dan Bashir ya ce, daga Annabi (SAW) – Hawwala Sanad- ya ce, “Aliyu dan Abdullahi ya ce, dan Uyainata ya ba mu labari daga Abu Farwat ya ce, Na ji Sha’abi ya ce, “Na ji Nu’aman dan Bashir (Allah Ya yarda da su) daga Annabi (SAW) – Hawwala Sanad – ya ce, “Muhammad dan Kasir ya ce, Sufiyan ya ba mu labari daga Abu Farwat daga Sha’abi daga Nu’aman dan Bashir (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Halal a bayyane take kuma haram a bayyane take a tsakaninsu akwai wasu abubuwa masu rikitarwa, duk wanda ya bar (kyale) abin da ya rikita masa daga laifi (zunubi), to ya kasance da wuya ya fada cikin laifi. Amma wanda ya fada cikin abin da ke da rikici cikinsa daga zunubi, to yana kusa ya fada cikin zunubi. Sabo iyakar Allah ce, wanda duk ya yi kiwo a gefen iyaka to yana kusan fadawa cikinsa (iyakar).”

Babi na Hudu: Fassarar rikitattun al’amura (masu kama da juna). Hassan dan Abu Sinan ya ce, “Ban ga abin da ya fi wannan magana tsantseni ba, cewa: Bar abin da kake kokwanto (shakka) ka koma ga abin da ba ka kokwanto.”
507. An karbo daga Muhammad dan Kasir ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Abdullahi dan Abdurrahman dan Abu Husain ya ce, Abdullahi dan Abu Mulaika ya ba mu labari daga Ukbatu dan Haris (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Hakika wata bakar mace ta zo ta riya cewa, ta shayar da su (nono shi da matarsa). Sai ya ambaci haka ga Annabi (SAW), sai Annabi (SAW) ya kawar da kai gabarinsa ya yi murmushi ya ce, “To yaya za ka yi, an riga an fadi (cewa an shayar da ku tare). Saboda matarsa ita ce ’yar Abu Ihabata Attamimi.