An karbo daga Isma’il ya ce:

353. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Nu’aim dan Abdullahi Mujmir daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “A bisa kowace kofar shiga Madina da akwai mala’ika, annoba da Dujal ba su shigarta.” 354. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya […]

An karbo daga Isma’il ya ce:
An karbo daga Isma’il ya ce:

353. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Nu’aim dan Abdullahi Mujmir daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “A bisa kowace kofar shiga Madina da akwai mala’ika, annoba da Dujal ba su shigarta.”

354. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Walid ya ba mu labari ya ce, Amru ya ba mu labari ya ce, Is’hak ya ba mu labari ya ce, “Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ba ni labari daga Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani gari face Dujal zai shige shi, sai dai Makka da Madina babu wata huji (kofa) daga kofofinsu face da mala’iku sun yi sahu suna tsaronsu. Sa’an nan Madina ta yi girgiza uku da mutanenta, sai Allah Ya fitar da da dukkan kafiri da munafikin cikinta.”

355. An karbo daga Yahya dan Kasir ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab ya ce, “Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utbah ya ba ni labari cewa: “Lallai Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ba mu labari da Hadisi mai tsawo game da Dujal abin da ya kasance ya ba mu labari da shi ya ce: “Dujalu zai zo alhali an haramta masa shiga kowace kafar (kofofin) Madina. Sai ya sauka a wasu wurare masu kanwa fako, sai ka ga mutum ya fito zuwa gare shi a wannan yini, alhali shi ne mafi alherin mutane, ko ya ce, fiyayyen mutane yana cewa: “Lallai na shaida kai ne Dujal wanda Manzon Allah (SAW) ya ba mu labarinka. Sai Dujal ya ce, “Shin ka gani idan na kashe wannan mutum na rayar da shi shin za ka yi shakka cikin al-amarin? Sai ya ce, “A’a, sai ya kashe shi, sa’annan ya rayar da da shi, sai ya ce, lokacin da ya rayarda shi: Wallahi babu wanda ya fini basira yau game da kai,” sai Dujal ya rika cewa: “Ina son kashe shi amma ban iyawa.”

 Babi na Goma: Madina na korar miyagun mutane:
356. An karbo daga Amru dan Abbas ya ce: “Abdurrahman ya ba mu labari ya ce, Sufiyan ya ba mu labari daga Muhammad dan Munkadir daga Jabir (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wani Balaraben kauye ya zo ga Annabi (SAW) ya yi masa mubaya’a a bisa Musulunci. Sai washegari ya komo da zazzabi ya ce da (Annabi): “Ka warware mini mubaya’ata,” (Annabi) ya ki karba masa haka har sau uku. Sai (Annabi) ya ce, “Madina kamar wutar makera take tana korar miyagun mutane kamar yadda wutar makera ke fitar da Daudarta. Kuma tana zabar (kyautata) mutanen kirkinta.”

357. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Adiyu dan Sabit daga Abdullahi dan Yazid ya ce: “Na ji Zaidu dan Sabit yana cewa: “Lokacin da Annabi (SAW) ya fita zuwa yakin Uhudu. Sai wasu daga cikin sahabbansa suka komo, sai wasu jama’a suka ce, “Sai mu yake su,” wasu kuma suka ce, “Kada mu yake su.” Sai wannan aya ta sauka da cewa: “Me ya faru da ku har kuke rabuwa kashi biyu saboda munafikai? (k:4:88).” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Lallai ita, Madina ta korar mutane miyagu kamar yadda wutar makera ke fitar da daudar bakin karfe.”