An karbo daga Yahya dan kaza’atu ya ce:
508. An karbo daga Yahya dan kaza’atu ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Urwatu dan Zubair daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Utbatu dan Abu Wakkas ya kasance ya yi alkawari wa dan uwansa Sa’ad dan Abu Wakkas da ya rike dan wata baiwa na kabilar Zama’a […]
508. An karbo daga Yahya dan kaza’atu ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Urwatu dan Zubair daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Utbatu dan Abu Wakkas ya kasance ya yi alkawari wa dan uwansa Sa’ad dan Abu Wakkas da ya rike dan wata baiwa na kabilar Zama’a a matsayin dansa (wato dan Utbah). Ta ce, “A shekarar da aka ci Makka da yaki ya kasance sai Sa’ad dan Abu Wakkas ya karbe shi ya ce, dan dan uwana ne a Jahiliyya wanda ya yi alkawari kansa. Sai Abdu dan Zama’ah ya mike ya ce, “dan uwana ne, dan baiwar babana wanda aka haifa bisa shimfidarsa. Sai suka tafi zuwa ga Annabi (SAW). Sa’ad ya ce, “Ya Manzon Allah! dan dan uwana ne wanda ya yi alkawari a kansa. Sai Abdu dan Zama’atu ya ce, “dan uwana ne, dan baiwar babana wanda aka haifa bisa shimfidarsa (gadonsa). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “dan uwanka ne, ya Abdu dan Zama’ah,” sa’an nan Annabi (SAW) ya ce, “da na shimfida ake tabbatarwa, amma mai tarawa (zina) da mace ba ya da komai face jifar dutse a kansa ga wanda ke da aure.” Sa’an nan ya ce, wa Saudatu ’yar Zama’atu matar Annabi (SAW) “Ki tsare kanki daga gare shi ya Saudah, lokacin da ya ga kamanninsa da Utba, bai sake ganinta (Saudatu ba) har sai da ya hadu da Allah.”
509. An karbo daga Abul Walid ya ce, “Shu’abah ya ba mu labari, ya ce, Abdullahi dan Abu Safar ya ba mu labari daga Sha’abi daga Addiyi dan Hatim (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Na tambayi Manzon Allah (SAW) game da magirbi (makami mai kaifi wanda ake harbin abin farauta da shi) sai (Annabi) ya ce, “Idan ya samu abin faruta da kaifinsa to kana iya ci. Amma idan ba da kaifin ya same shi ba, kada ka ci sai ka yanka, domin ya zamo kamar wanda aka jefe ke nan ya mutu. Na ce, “Ya Manzon Allah (SAW) ina aika wa da karena, sai in ambaci sunan Allah amma nakan iske shi da wani kare wanda ban ambaci sunan Allah ba a kansa, kuma ban san wanne ne daga cikinsu ya kama abin farautar ba. (Annabi) ya ce, “Kada ka ci, domin ka ambaci sunan Allah ne, bisa kan karenka amma ba ka ambaci sunan Allah a kan daya karen ba.”
Babi na Biyar: Abinda ake nesanta (tsarkaka) daga abubuwa masu rikici:
510. An karbo daga kabisatu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Mansur daga dalhat daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Annabi (SAW) ya shude da wani dabino wanda ya fadi. Sai ya ce, “Ba domin ina jin tsoron kada ta kasance na sadaka ba, da na ci (saboda Annabi ba ya cin sadaka).” Hammam ya ce, “Daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce, “Ina samun dabino wanda ya fadi bisa shimfidata,” (sai in bar shi saboda tsoron ko na sadaka ne).