An karrama Amitabh Bachchan a Indiya

A ranar Asabar da ta gabata ne aka karrama fitaccen jarumin fina-finan Indiya Amitabh Bachchan da lambar yabo ta Akkineni Nageswara Rao (ANR) sakamakon gudunmuwar da ya ba harkar fim a Indiya. An kirkiro wannan bikin karramawar ne don karrama masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Indiya sakamakon gudunmuwar ci gaba da suka ba […]

An karrama Amitabh Bachchan a Indiya
An karrama Amitabh Bachchan a Indiya

A ranar Asabar da ta gabata ne aka karrama fitaccen jarumin fina-finan Indiya Amitabh Bachchan da lambar yabo ta Akkineni Nageswara Rao (ANR) sakamakon gudunmuwar da ya ba harkar fim a Indiya.
An kirkiro wannan bikin karramawar ne don karrama masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Indiya sakamakon gudunmuwar ci gaba da suka ba masana’antar.
Bayan ya karbi kyautar sai ya ce: “Abin alfahari ne da na kasance cikin wannan masana’anta. Ina farin ciki da wannan kyautar domin zakakurai irinsu marigayi ANR ne suka kare mutuncin wannan masana’anta. Saboda shi wannan masana’anta ta tsaya da kafafunta.”
dan marigayi jarumi Nageswara Rao mai suna Akkineni Nagarjuna ya gode wa Amitabh Bachchan da ya karbi wannan kyautar.
&nbsp K. Chandrasekhar Rao da Ministan harkokin cikin gida na kasar Indiya benkaiah Naidu da masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan Indiya.
An fara wannan bikin karramawa na ANR a shekarar 2005. A cikin wadanda aka taba ba kyautar akwai Deb Anand da Shabana Azmi da Anjali Debi da byjayanatimala Bali da Lata Mangeshkar da K. Balachander da Hema Malini da kuma Shyam Benegal.